Kasashen Afrika 7 Da Ke a Karkashin Mulkin Soji Yayin Da Sojoji Suka Amshe Mulki a Kasar Gabon
- Dimokuraɗiyya a Afrika na fuskantar ƙalubale da dama duk da irin ci gaban fasahohi da aka samu
- A yanzu haka ƙasashe bakwai na Afrika ne ke a ƙarƙashin mulkin soji a shekarar 2023 da muke ciki
- Daga baya-bayan nan ne dai aka ƙara samun ƙarin ƙasashen da sojoji suka amshe mulki daga hannun farar hula
Tarihin ƙasashen Afrika ba zai cika ba, idan ba a kawo labarin juyin mulkin da aka yi a can baya ba wanda kuma har yanzu yake ci gaba da wanzuwa har a wannan lokacin da ake ciki.
Ƙasashen Afrika ta Yamma ne suka fi fuskantar ƙalubalen juyin mulki tun bayan dawowa turbar dimokuraɗiyya.
Mulkin farar hula a ƙasashen Afrika cike yake da cin hanci da rashawa, son rai, ƙabilanci, addinanci da kuma ɓangaranci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin kasashen Afrika 7 da ke a ƙarƙashin juyin mulki
1. Burkina Faso
Sojoji sun amshe mulki hannun farar hula a ƙasar Burkina Faso, wacce rainon ƙasar Faransa ce tun a shekarar 2022.
Rahoton bankin duniya ya nuna cewa Burkina Faso na da yawan mutane da suka kai miliyan 22.1, kuma ta haɗa iyaka da ƙasashen Mali, Nijar, Benin, Togo, Ghana da Kwaddibuwa.
Kasar na ƙarƙashin mulkin matashin soja ɗan shekara 34 mai suna Ibrahim Traoré.
2. Chad
Kasar Chad ƙasa ce ta Arewacin Afrika da ta haɗa iyaka da ƙasashen Libya, Sudan, Afrika ta tsakiya, Kamaru, Najeriya da kuma Nijar.
Mahamat Idriss Déby ne ke shugabantar ƙasar, wacce take da yawan mutane da suka kai aƙalla miliyan 17.18.
3. Guinea
Kasar Guinea ma wata ƙasa ce ta Afrika ta Yamma da ke a hannun soji ƙarƙashin jagorancin Mamady Doumbouya tun a shekarar 2021.
Ƙasar Guinea dai na da yawan mutane da suka kai miliyan 13.53.
4. Mali
Kasar Mali ma na daga cikin ƙasashen Afrika ta Yamma da ta kasance cikin rainon ƙasar Faransa da sojoji suka amshe mulki.
Assimi Goïta, mai kimanin shekaru 42 ne ke jagorantar ƙasar a ƙarƙashin mulkin soji tun a shekarar 2020.
5. Niger
Jamhuriyar Nijar tana cikin na baya-bayan nan da sojoji suka kifar da farar hula sannan suka ɗare kan karagar mulki.
A ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023 ne shugaban dakarun tsaron shugaba Bazoum, Janar Abdourahmane Tchiani ya sanar da hamɓarar da gwamnatin Nijar mai ci.
Hakan ya janyo cece-kuce da suka daga sassa daban-daban na duniya, ciki kuwa harda ƙungiyar ECOWAS wacce ta ƙaƙabawa sojojin na Nijar takunkumi.
6. Sudan
Sudan na daga cikin ƙasashen Arewacin Afrika da ke a ƙarƙashin mulkin soji tun a shekarar 2021.
A yanzu haka Janar Abdel Fattah al-Burhan ne ke jagorantar ƙasar a mulkin soji.
7. Gabon
Da safiyar ranar Laraba, 30 ga watan Agustan 2023 ne aka wayi gari da sanarwar ƙwace mulki da sojojin Gabon suka fitar a gidan talabijin na ƙasar.
Hakan na zuwa ne jim kaɗan bayan kammala zaɓen ƙasar ta Gabon, inda Shugaba Ali Bongo ya sake komawa a karo na uku.
A wani rahoto da kafar Aljazeera ta fitar, an bayyana cewa har yanzu gwamnatin ƙasar ba ta ce komai ba dangane da batun juyin mulkin.
Janar Tchiani zai maidawa farar hula mulki bayan shekara uku
A wani labarin na daban da Legit.ng ta wallafa a baya, shugaban mulkin sojin jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya bayyana cewa za su mayar da mulki hannun farar hula bayan shekara uku.
Janar Tchiani ya bayyana cewa zai kafa kwamitin da zai sake yin garambawul ga kundin tsarin mulkin ƙasa.
Asali: Legit.ng