Sojojin Juyin Mulkin Nijar Sun Yi Fatali Da Bukatar ECOWAS Ta Su Bar Mulki
- Sojojin da suka jagoranci kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a Jamhuriyar Nijar sun yi fatali da buƙatar ƙungiyar ECOWAS
- Sojojin sun kuma gargaɗi ƙungiyar da ƙasashen Yamma kan yin amfani da ƙarfin soja wajen kawar da su daga kan mulki
- Ƙungiyar ECOWAS dai ta ba sojojin wa'adin kwana bakwai domin su bar mulki tare da sakin Shugaba Bazoum da mayar da shi kan muƙaminsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) a ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja, ta ba sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin Shugaba Bazoum a Jamhuriyar Nijar wa'adin kwana bakwai su bar madafun iko.
Ƙungiyar ta ECOWAS ta kuma umarci sojojin da su gaggauta sakin Shugaba Mohamed Bazoum tare da mayar da shi kan muƙamin shugabancin Jamhuriyar Nijar, cewar rahoton Thisday.
Sai dai, a wani martani cikin gaggawa, sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin sun yi watsi da kiran na ƙungiyar ECOWAS tare da jan kunnen ƙungiyar da kada ta yi tunanin yin amfani da ƙarfin soji, rahoton The Punch ya tabbatar.
Sojojin sun ja kunnen ƙungiyar ECOWAS
Sojojin sun gargaɗi ƙungiyar cewa a shirye su ke su kare ƙasarsu ta haihuwa akan duk wani wanda ka iya kawo mata hari.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A wani bayani da sojojin suka fitar a gidan talabijin na ƙasar, sojojin sun yi gargaɗi kan yin amfani da ƙarfin soji a ƙasar.
Kakakin sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin, Kanal Amadou Abdramane ya bayyana cewa:
"Manufar taron ECOWAS shi ne amincewa da shirin tsokanar Jamhuriyar Nijar ta hanyar yin amfani da ƙarfin soja tare da haɗin gwiwa da sauran ƙasashen Afirika waɗanda ba mambobin ECOWAS ba, da wasu ƙasashen Yamma."
Janar Tchiani: Muhimman Abubuwan Sani Guda 5 Dangane Da Sojan Da Ya Kitsa Hambarar Da Gwamnati a Jamhuriyar Nijar
"Muna son mu sake tunatar da ECOWAS da sauran ƴan kanzagi cewa a shirye mu ke mu kare ƙasar mu ta haihuwa."
Matakan da ECOWAS da AU za su ɗauka akan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar
Daga cikin matsayar da ƙungiyoyin suka cimmawa sun haɗa da kulle iyakokin sama da na ƙasa na ƙasashen dake makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, rahoton The Nation ya tabbatar.
Dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da soke dukkanin harkokin cinikayya da tallafi, tare da kulle dukkanin asusun ajiya na banki da ƙwace kadarorin ƙasar.
Sanya takunkumin yin tafiya ga jami'aan sojojin da iyalansu da amfani da ƙarfin soja a kan sojojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum.
ECOWAS Za Ta Yi Amfani Da Karfin Soja
A wani labarin kuma, ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) ta gargaɗi sojojin da suka jagoranci hamɓarar da mukin farar hula a jamhuriyar Nijar da su gaggauta barin mulki
Ƙungiyar ta nuna shirinta na yin amfani da ƙarfin soja idan har sojojin ba su bi umarnin da ta ba su ba na barin muki tare da mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan muƙaminsa.
Asali: Legit.ng