Fasto Ya Mutu Sa'o'i Kadan Bayan Ya Je Otal Tare Da Budurwarsa
- Wani faston ɗariƙar Katolika ya yi bankwana da duniya bayan ya je otal cin duniya da tsinke tare da masoyiyarsa
- Fasto Joseph Kariuki Wanjiku mai shekara 43 a duniya ya kama ɗaki ne a otal ɗin da yammacin ranar Juma'a
- Sai dai, faston ya mutu ne da safiyar ranar Asabar bayan ya kwashe wasu sa'o'i a otal ɗin tare da budurwarsa
Nairobi, Kenya - Wani faston ɗariƙar Katolika mai shekara 43 a duniya ya mutu sa'o'i kaɗan bayan shi da masoyiyarsa sun je otal.
Jaridar The Punch tace faston mai suna Joseph Kariuki Wanjiku na cocin St. Peters Ruai, yaje otal ɗin Monalisa Hotel Delview a Gatanga tare da masoyiyarsa mai suna Ruth Nduhi mai shekara 32 da yammacin ranar Juma'a.
A cewar rahoton ƴan sanda budurwar ta gayawa shugabannin otal ɗin da safiyar ranar Asabar cewa faston yana ganin jiri inda yake fita hayyacinsa.
Nan da nan suka garzaya da shi cikin motarsa zuwa asibitin Kenol a Murang'a domin duba lafiyarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An tabbatar da mutuwar fasto Joseph Kariuki
Faston ya yi bankwana da duniya ne yana cikin motarsa wacce aka yi amfni da ita domin kai shi zuwa asibiti
Jami'an ƴan sandan da aka kira zuwa wajen sun samu gawar faston a kujerar baya ta motar tare da bargon otal ɗin da farar kumfa tana fitowa ta bakinsa da hancinsa, cewar rahoton Pulselive.co.ke
Mutuwar kwatsam da faston ya yi ta janyo ana ta zarge-zarge, wanda hakan ya sanya hukumomi suka fara gudanar da bincike kan musabbabin mutuwarsa.
An kai gawarsa zuwa ɗakin ajiyar gawa na asibitin Mater a bisa rakiyar jami'in ɗan sanda inda ake jiran sakamakon binciken gawar." Cewar rahoton ƴan sanda.
Abinci da kayan shan da masoyan biyu suka yi ta'ammali da su a cikin daren, an tafi da su domin duba su yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.
Fasto Mai Kwaikwayon Azumin Yesu Ya Mutu
A wani labarin na daban kuma, wani fasto ya mutu ya bar duniya bayan ya kuɗiri aniyar kwaikwayon irin azumin da Yesu ya yi.
Faston ɗan ƙasar Mozambique ya koma daji ya tare har sai ya yi azumin kwanaki 50 kamar yadda Yesu ya yi. Sai dai, bai kai labari ba inda ya mutu yana tsaka da azumin.
Asali: Legit.ng