An Tabbatar Da Rasuwar Duka Mutane 5 Da Ke Cikin Jirgin Ruwan Titan Da Ya Bace A Tekun Atlantika
- An tabbatar da cewa mutanen da ke cikin jirgin ruwa mai ninƙaya Titan, sun riga mu gidan gaskiya
- Jirgin yana ɗauke da mutane biyar waɗanda ke kan hanyarsu ta zuwa yawon buɗe ido a cikin tekun Atlantika
- Mutanen sun rasu ne a yayin da suke ƙoƙarin zuwa wurin da ɓaraguzan jirgin Titanic da ya yi haɗari shekaru 111 da suka wuce
An tabbatar da mutuwar mutane biyar ɗin da ke cikin jirgin ruwan Titan, wanda jirgi ne na sunduƙi mai nutsewa a cikin ruwa.
Jami'in yada labaran kamfanin jirgin na OceanGate Expeditions, Andrew Von Kerens ne ya tabbatar da labarin a ranar Alhamis, 22 ga watan Yunin 2023, wanda kuma aka wallafa a shafin kamfanin na Tuwita.
Mutanen sun rasa ransu ne a yayin da suke yunƙurin ziyartar inda buraguzan jirgin Titanic suke a ƙasan teku, a cikin wata tafiya ta yawon buɗe idanu a jirgin, wanda yake mallakin wani kamfani ne mai suna OceanGate.
An bayyana sunayen waɗanda ke cikin jirgin da Hamish Harding, Shahzada Dawood, Suleman Dawood, Paul-Henri Nargeolet, da kuma Stockton Rush, mai kamfanin na OceanGate.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar wani bangare na sanarwar:
"Yanzu mun yi imanin cewa shugabanmu Stockton Rush, Shahzada Dawood da dansa Suleman Dawood, Hamish Harding, da Paul-Henri Nargeolet, sun riga da sun rasu."
Jirgin Titanic, wani jirgin ruwa ne da ya nutse a haɗarin da ya gamu da shi shekaru 111 da suka gabata a tekun atlantika.
A ranar Lahadin da ta gabata ne, jirgin na 'yan yawon buɗe ido Titan, wanda mallakin kamfanin OceanGate ne ya yi nunƙaya a ƙasan tekun atlantika.
Sai dai ba a wuce sa'o'i biyu da yin wannan nunƙaya da jirgin ya yi ba, aka daina jin ɗuriyarsa.
Hankula sun tashi inda nan da nan hukumomin agaji daban-daban da haɗin gwiwar jami'an tsaron teku na ƙasar Amurka, wato US Coast Guard, suka bazama neman jirgin.
'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Cikin Tsakar Dare a Wata Jiha, Rayukan Mutane Da Dama Sun Salwanta
An gano ɓaraguzan jirgin na Titan
An shafe kwanaki aƙalla huɗu ana neman jirgin ruwan na Titan, wanda ba a iya ganosa ba har sai zuwa ranar Alhamis da jami'an tsaron tekun na ƙasar Amurka suka iya gano wasu ɓangarori na jikin jirgin, kamar yadda CBS News ta wallafa.
John Mauger, babban jami'in tsaro gaɓar tekun na Amurka, ya shaidawa manema labarai cewa an gano wasu bangarori na jirgin a kusa da ɓaraguzan jirgin Titanic da ya yi haɗari sama da shekaru 100 da suka wuce.
An yi amfani da wata na'ura da aka tura kasan tekun, wacce ake sarrafawa daga waje, a yayin gano bangarorin jirgin.
An bayyana cewa kowane daga cikin 'yan yawon buɗe idon ya biya dalar Amurka 250,000 domin zuwa kallon ɓuraguzan jirgin Titanic da ke kusan ƙafa 13,000 a ƙasan tekun Atlantika.
Mutane 40 sun nutse a wani haɗarin jirgin ruwa a Sokoto
A wani labari da Legit.ng ta kawo muku a baya, mutane 40 waɗanda dukkansu 'yan matane suka nutse a wani haɗarin kwale-kwale da ya auku a jihar Sokoto.
An bayyana cewa 'yan matan sun fito ne daga ƙauyen Dundeji, za su je Kambama da ke ƙaramar hukumar Shagari da zummar samo iccen girki.
Asali: Legit.ng