Fitaccen Mawakin Amurka, Big Pokey, Ya Sheka Barzahu A Yayin Da Yake Cashewa
- Wani fitaccen mawaƙi ɗan asalin birnin Houston da ke Amurka ya yanke jiki ya faɗi a sanda yake tsaka da waƙa
- Mutane da dama da ke a wurin da lamarin ta faru sun yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen ganin sun ceci rayuwarsa
- An tabbatar da mutuwar mawaƙin, bayan garzawa asibiti da aka yi da shi, domin likitoci su yi iya bakin nasu aikin
Wani fitaccen mawakin Amurka mai suna Milton Powell wanda aka fi sani da sunansa na waƙa Big Pokey, ya yanke jiki ya faɗi a lokacin da yake nishaɗantar da masoyansa.
A cikin wani faifan bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, an ga Pokey riƙe da makirho yana magana, kwatsam sai aka ga ya faɗi ta baya warwas a ƙasa.
Jami'in tsaron da ke wurin da ma wasu daga cikin masoyansa sun rugo da gudu da nufin su taimaka masa a lokacin da ya ke kwance magashiyyan.
Abinda ya faru da mawaƙin bayan faɗuwar da ya yi
Bayan faruwar lamarin, bidiyon mawakin, ɗan kimanin shekaru 48, a lokacin da ya faɗi, ya yaɗu sosai a kafafen sada zumunta.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Fox 26 ta ce bayan faɗuwar mawaƙin, an yi ƙoƙarin garzayawa da shi asibiti, inda likitoci suka yi ƙoƙarin ba shi agajin gaggawa.
Daga cikin abubuwan da likitocin suka yi masa hadda dannar ƙirji (CPR), da ake yi wa mutum a yayin ɗaukewar numfashi.
Sai dai duk da irin abubuwan da aka yi a asibitin, mawaƙin bai haye ba, inda daga bisani ya ce ga garinku nan.
Masoyan Big Pokey sun nuna alhini a kafafen sada zumunta
Masoyansa da wasu daga cikin abokan sana'arsa sun wallafa hotunsa da gajerun bidiyoyinsa a shafukan sada zumunta domin nuna alhini.
Wani abokinsa mai suna Paul Wall Baby, ya ɗora wani ɗan guntun bidiyo na yabon mamacin a shafinsa na Instagram.
A cikin ɗan gajeren bidiyon, an nuna mawaƙi Big Pokey yana nishaɗantar da tarin masoyansa a cikin wani ɗakin taro.
Kafin mutuwarsa, Big Pokey ya kasance shahararren mawaƙi ɗan asalin birnin Houston da ke ƙasar Amurka.
An lakaɗawa mawaƙi duk saboda ya ƙi rerawa ɗan takarar waƙa
Wani labari da Legit.ng ta kawo muku a kwanakin baya, shi ne na wani mawaƙi Kelvin Ibinabo da aka lakaɗawa dukan tsiya kan ƙi yi wa wani ɗan takara waƙar siyasa.
Mawaƙin ya zargi hadimin wani ɗan takarar gwamna, da sanya 'yan daban su lakaɗa masa dukan kawo wuƙa.
Asali: Legit.ng