Satar Fukafukin Kaza Da Man Gyada: An Yanke Wa Wasu Ma'aikata Biyu Daurin Shekara 5 A Gidan Yari

Satar Fukafukin Kaza Da Man Gyada: An Yanke Wa Wasu Ma'aikata Biyu Daurin Shekara 5 A Gidan Yari

  • An samu Sa'idu Karim da Rashid Abdullahi da laifin satar kwali 20 na naman kaji da kuma litocin man girki a gidan abincin Pizzaman
  • Sukan saci kayayyakin ne su ɓoye daga baya kuma sai su je su ɗauka su yi gaba
  • Gidan abincin ya kai su ƙara kotu domin a yanke musu hukunci kan laifin da suka aikata

An tura wasu ma'aikatan gidan abincin Pizzaman su biyu Sa'idu Karim da Rashid Abdullahi gidan yari na tsawon shekara 5 saboda satar kwali 20 na fukafukin kaji da kuma man girki a gidan abincin da su ke aiki da ke Nyankyerenease, Kumasi, da ke ƙasar Ghana.

Jami'i mai shigar da ƙara ASP, Jonas Newlove Adjei ya shaida ma alƙalin da ke gabatar da shari'ar cewa an kira babban kukun gidan abincin daga can inda su ke yin ajiye-ajiye inda ake shaida mishi cewa an sace kwali takwas na fuka-fukan kajin da kuma litocin man girki biyu.

Kara karanta wannan

Tashin Hankalin Da Muka Shiga a Sudan Ba Ɗan Kaɗan Ba Ne, In Ji Ɗalibi Bello Halliru

Saidu and Rashid
Kotu Ta Yanke Wa Rashid da Saidu Hukuncin Shekara 5 Saboda Satar Fukafukin Kaji. Hoto: Tribune
Asali: UGC

Gidan abincin ya kira taro na gaggawa

Kukun ya ce bayan da aka sanar da shi sai ya yi ƙoƙarin zuwa inda ake ajiye kayayyakin da ake amfani da su yau da kullum a gidan abincin na Pizzaman. Zuwan shi ke da wuya sai ya tarar da an kwashe kayayyakin jaridar Tribune ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Faruwar hakan ke da wuya sai aka kira taron ma'aikata na gaggawa a gidan abincin sannan kuma aka buƙaci ma'aikatan da ake zargi da su fito da kayayyakin da su ka ɗauka.

An samu kayayyakin a gurin wadanda ake tuhuma

A gurin ne Rashid Abdullahi ya bayyana cewa ya ga lokacin da Sa'idu Karim ya ke ɓoye lita biyu na man Oki da ya sata a bayan wani shinge. A ƙoƙarin ya kare kan shi daga laifin da ake tuhumar shi, Sa'idu Karim ya ce shima ya ga lokacin da Rashid Abdullahi ya ke ƙoƙarin ɓoye wasu fuka-fukan kaji a gefen katangar shingen.

Kara karanta wannan

Yadda Kasar Masar Ta Umarci Ɗaliban Najeriya Sama da 500 Su Koma Sudan Kan Halayyar Mutum 2

Daga ƙarshe dai an samu nasarar samo kayayyakin da aka sace ɗin daga wajen su sannan kuma aka miƙa su a hannun 'yan sanda. A yayin binciken ne Sa'idu Karim ya amsa cewa ya sami lita 20 na man girki.

Na janye batun da nayi na cewa zanyi hijira in Tinubu ya ci

A wani labarin kuma, tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Legas ta ce ta janye batun da ta yi a can da na cewar muddun Tinubu ne ya ci zaɓen shugaban ƙasa to za ta yi hijira daga Najeriya zuwa wata ƙasar.

Ta ce koyarwar addinin Musulunci ce ta sanya ta sauya ra'ayi dangane da iƙirarin da ta yi a farko. Sannan kuma ta ce akwai mutane da dama da ta ke ganin girman su da su ka ba ta baki akan ta janye maganar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng