Bayan Shekaru Fiye Da 30 Yana Jogorantar Sallah, Shuraim Ya Yi Bankwana Da Limanci A Masallacin Makkah
- Daya cikin limaman dindindin na masallacin Harami da ke Makka, Sheikh Saud Ash Shuraim ya yi bankwana da limanci
- Hakan ta tabbata ne biyo bayan fitar da sunayen limaman da za su jagoranci sallar Tarawi na azumin bana kuma babu sunansa
- A yan kwanakin baya, Sheikh Shuraim ya nemi a bashi uzurin yin murabus din da aka ce ya nema don kashin kansa
Saudiyya - Yanzu babu sauran shakku kan cewa Sheikh Saud Ash Shuraim ya dena limanci a mallacin Ka'abbah da ke kasar mai tsarki ta Saudiyya, rahoton BBC Hausa.
An tabbatar da hakan ne yayin da hukumar da ke kula da masallatai mafiya tsarki biyu na duniya wato masallacin Makkah da Madina ta saki jerin sunayen limaman da za su jagoranci sallar Tarawi, amma sunasa ba ya ciki.
A baya, tun dai a watan Janairu rahotanni sun fito da ke cewa limami guda daya cikin shahararrun limaman manyan masallatan biyu zai ajiye aiki.
Sai dai a watan Fabrairun 2023 ne bayanai suka fito fili cewa Sheikh Saud Ash Shuraim ne limamin da zai ajiye aiki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Fitaccen limamin ya yi kimamin shekaru 32 yana jagorantar sallah a Saudiyya.
A ranar 12 ga watan Rabi Al Awal na 1443 wato Litinin 18 ga watan Oktoban shekarar 2021 ne Shuraim ya ja sallarsa ta karshe a masallacin Ka'abah.
Abin da yasa Shuraim ya yi murabus
A hukumance ba a sanar da dalilin da yasa babban limamin ya ajiye aiki ba duk da cewa yana da sauran karfinsa, sai dai wasu kafofi sun rahoto cewa shi da kansa ne ya bukaci zai dena limancin.
Takaitaccen tarihin Shuraim
Bayanai sun nuna cewa an haifi Sheikh Sa’ud Ibn Ibrahim Ibn Muhammad Al-Shuraim a ranar 19 ga watan Janairun 1964 a Riyadh, Saudiyya.
Ya yi karatun firamare a Areen Elementary School ya kuma yi sakandare a Modern School for Secondary Education.
Daga bisani ya cigaba da karatun sakandare a Al-Yarmouk North High School, ya kammala a 1983.
Ta tafi jami'ar Imam Muhammad Bin Saud, ya yi digiri a 1988.
Bai tsaya nan ba, ya cigaba da zurfafa karatu har sai da ya samu digirin digirgir.
An Bude Birnin At-Turaif A Saudiyya
A wani rahoton, kun samu rahoto cewa a ranar 4 ga watan Disamban 2022, Saudiyya ta sanar da bude tsohon birni mai tarihi na At-Turaif.
Kamar yadda BBC Hausa ta rahoto, za a bude birnin ne domin mutane masu zuwa yawon bude ido wadanda ke sha'awan tarihin kasar.
Asali: Legit.ng