Namibia: Kasar Dake da Mutane 2.5m amma Ake Amfani da Kwaroron Roba 45m a Shekara

Namibia: Kasar Dake da Mutane 2.5m amma Ake Amfani da Kwaroron Roba 45m a Shekara

  • Jimillan mutane 2.5 miliyan ke kasar amma mazan Namibian 726,000 ne suke amfani da kwaroron roba 45 miliyan a duk shekara
  • An tabbatar da hakan ne a wani rahoto da ma'aikatar lafiya ta Namibia ta fitar cikin kwanakin nan
  • Ministan lafiya, Kalumbi Shangula, shima ya bayyana yadda kusan kashi 13 na 'yan kasar ke dauke da cutar kanjamau

Ma'aikatar lafiya ta Namibia ta saki sabon rahoton da ke bayyana yadda aka amfani da kwaroron roba miliyan 45 a duk shekara a fadin kasar.

Kalumbi Shangula
Namibia: Kasar Dake da Mutane 2.5m amma Ake Amfani da Kwaroron Roba 45m a Shekara. Hoto daga Kalumbi Shanbula
Asali: UGC

Daraktan lafiya Ben Nangombe ya bayyana cewa maza 726,000 cikin jimillar 'yan kasar 2.5 miliyan suke amfani da kwaroron roba 45 miliyan duk shekara.

Ministan lafiya na Namibia, Kalumbi Shangula ya ce a kalla kashi 13 na 'yan kasar ke dauke da cutar kanjamau.

Ya sanar da hakan ne a wata zantawa da manema labarai da ya yi kwanan nan yayin bayyana yadda kanjamau ya yi yawa a kasar.

Kara karanta wannan

Sauya Fasalin Naira: Kashi 80% Na Masu Sana'ar POS Sun Kare, Kungiyar Masu POS

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Hakan na nufin ana bukatar kwararon roba 37.8 miliyan masu girman 52 millimeter a fadin kasar.”

- A cewarsa.

Nangombe ya bayyana cewa lafiyayyun maza 726180 a kiyasin da akai suke bukatar kwararon roba 40 kowannensu duk shekaram.

Hakan ya danganta da yawan 'yan kasar 2.6 miliyan, wanda 49% maza ne, inda kusan maza 1.2 miliyan ne na gaba daya 'yan kasar, kashi 57 sune ke tsakanin shekaru 15 zuwa 64, wanda ita ce shekarun samun haihuwa.

Sai dai, ministan lafiya na Namibia, Kalumbi Shangula ya bayyana yadda a kalla sama da mutane 33,000 ke rayuwa da cutar kanjamau ba tare da sun san suna da cutar ba balle su kula da lafiyarsu.

A cewarsa, hakan ya janyo jaduwar cutar ta hanyar shayarwan da uwa ke wa jinjiri, wanda kimanin mutane 219,000 suke kamu da cutar ta wannan hanyar.

Kara karanta wannan

Jami’an NDLEA Sun Kama Mata Mai Juna Biyu Da Miyagun Kwayoyi A Cikin Rediyo

A cewarsa:

"Mutane da dama da ke dauke da cutar HIV suna shan magani kullum kuma suna cikin koshin lafiya.
"Ba tare da daukar tsauraran matakan kiyaye kai daga HIV ba, annobar zata cigaba da yaduwa ba tare da misali ba."

A cewarsa:

“Yawan mace-mace da jama'an da ke dauke da cutar HIV ya fi rabi. Yawan kamuwa da cutar HIV yafi sau hudu.
"Yawan kamuwar cutar kanjamau ga yara ya rage da kashi 90.
“Asibitoci sun dai na damuwa da cutar HIV."

Matar aure ta haifa jinjiri da IUD a hannu

A wani labari na daban, wata matar aure mai suna Violet ta bayyana yadda ta dauka juna biyu duk da tsarin iyalin da ta ke yi.

Tayi bayanin cewa, ta haifa yaronta namiji rike da IUD a hannu, lamarin da ya matukar girgiza ma'aikatan asibitin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng