Elon Musk ya Kafa Tarihi, Ya Zama Mutum na Farko a Duniya Da Yayi Asarar $200bn Daga $320bn

Elon Musk ya Kafa Tarihi, Ya Zama Mutum na Farko a Duniya Da Yayi Asarar $200bn Daga $320bn

  • Elon Musk ya kafa tarihi a matsayin mutum na farko da ya tafka babbar asarar dukiya ta $200 biliyan a shekara daya
  • Farkon shekarar 2022, mai kamfanin Tesla na da jimillar dukiya ta $320 biliyan wacce yayi asararta a shekara daya
  • A halin yanzu yana da jimillar dukiya ta $132 biliyan, sannan ya rasa matsayinsa na wanda yafi kowa kudi a duniya

Mai kamfanin Tesla, Elon Musk ya zama mutum na farko sannan tilo da ya tara kuma yayi asarar $200 biliyan a tarihin bil'adama.

Yanzu haka yana kasa da attajirin bafuransan nan, Bernard Arnault mai jimillar dukiya ta $137 biliyan, kamar yadda Bloomberg Billionaire ta kididdiga.

Elon Musk
Elon Musk ya Kafa Tarihi, Ya Zama Mutum na Farko a Duniya Da Yayi Asarar $200bn Daga $320bn. Hoto daga JIM WATSON / Contributor
Asali: Getty Images

Ana tunanin mayar da hankali da yayi a kasuwancinsa na Twitter ne ya janyo rasa hannayen jarinsa naTesla. Cikin kwanakin nan, mai kamfanin SpaceX ya siyar da hannayen jarinsa da dama na Tesla cikin shekarar.

Kara karanta wannan

An Yi Girman Banza: Bidiyon Yadda Matashi Ya Rusa Kuka da Hawaye Saboda Budurwarsa Tace Su Rabu

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, ya siyar da kimanin kayayyaki na $32 biliyan na Tesla a shekarar 2022 wanda mutane da dama suke ganin ya narka a Twitter.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A yanzu, jimillar dukiyarsa ta SpaceX ta kai $44.8 biliyan, wacce ta haura matsayinsa na mai jimillar dukiyar $44 biliyan na hannayen jarin Tesla.

Wanda $320 biliyan ta kusan bacewa, Musk ya daga zuwa jerin manyan biloniyoyin duniya ne lokacin da arzikinsa ya kai $340 biliyan a 2021. Ya rasa matsayinsa na attajirin da yafi kowa dukiya a farkon Disamba ga Arnault.

Da zafi ya karba ragamar Twitter

Ya fara kasuwancin Twitter cikin kaushi inda ya kori sama da ma'aikatan Twitter 7,000, wanda hakan yayi sanadin dakatar da tallace-tallace a kafar sada zumuntar. Twitter ta fuskanci matsanantanciyar asara a tattalin arzikin tun daga lokacin da Musk ya karbi ragamar.

Kara karanta wannan

Allah Mai Zamani: Biloniyan Farko na AFrika Yanzu Yana Kasa da Dangote da 881 a Duniya

Ya kirkiro da tsarin biyan kudi ga dukkan shafukan kafar wanda mutane da dama suka saki hakan. Biloniyan ya janye hannun jarin Tesla da ya fadi gami da sukar hukumar tarayyar US kan kara haraji, wanda ya dora laifin ga hannun jarin Tesla bisa karin.

Elon Musk ya taya Twitter, zai siye ta dugurungum

A wani labari na daban da Legit.ng ta kawo, ta bayyana cewa Elon Musk, hamshakin mai arzikin duniya ya taya Twitter baki daya.

Zai siye ta kan kudi har dala biliyan 43 bayan yardar da yayi cewa wuri ne da ya dace ya zama mallakin mutum daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng