Patrice Motsepe: Biloniya na Farko a Afrika Wanda Yanzu Dangote Yayi Masa Tazarar Sama da Kasa

Patrice Motsepe: Biloniya na Farko a Afrika Wanda Yanzu Dangote Yayi Masa Tazarar Sama da Kasa

  • Patrice Motsepe, wani biloniyan kudancin Afirka wanda shine bakar fata na farko da ya shiga jerin sunayen biloniyoyin Forbes
  • Kamar yadda Forbes ta bayyana Motsepe a yanzu yana da kadara mai kimar dalar Amurka 2.6 biliyan sannan shine mutum na 1023 a jerin masu kudin duniya
  • Motsepe a halin yanzu shine na 881 baya ga Dangote wanda shine na 142 a jerin sunayen biloniyoyin da Forbes ta bayyana a duniya

Patrice Motsepe wani biloniyan kasar Afirka ta Kudu ne mai jimillar $2.8 biliyan kamar yadda aka bayyana a ranar Lahadi 25 ga watan Disamba 2022. A shekarar 2005, shi ne ya zamo bakar fata na farko da ya leko a jerin sunayen biloniyoyin duniya yana da shekaru 46.

Patrice Motsepe
Patrice Motsepe: Biloniya na Farko a Afrika Wanda Yanzu Dangote Yayi Masa Tazarar Sama da Kasa. Hoto daga Bloomberg
Asali: Facebook

A yanzu, Motsepe shi ne mutum na 1023 a jerin attajiran duniya, mataki na 881 kasa da Aliko Dangote wanda shi ne na 142 a jerin sunayen da jimillar dukiya $12.6 biliyan.

Kara karanta wannan

Assha: An kama basarake a babban masarautar Arewa bisa zargin lalata da yaro karami

Forbes ta ruwaito yadda tumbatsar dukiyar Motsepe ta samo asali ne daga mallaka gami da zama shugaban Rainbow Minerals, wani kamfani mallakinsa da ya bude a 2016.

Haka zalika, Motsepe nada hannun jari a Sanlam, wani kamfanin narka hannun jari, kuma shine shugaban sannan mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Mamelodi Sondowns.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Attajirin ya fito ne daga dangin 'yan kasuwa, wanda haka yasa kasuwancinsa ya zama kamar gado. Kakansa da mahaifinsa duk 'yan kasuwa ne.

Mahaifinsa, wanda sarkin yankin Mmakau ne na mutanen Tswana lokacin da yana raye, malamin makaranta ne daga baya ya koma harkar kasuwanci a matsayin mamallakin kantin Spaza wanda mahakan ma'adanai suka fi zuwa siyan kayan aiki.

Daga nan ne Motsepe ya samu wayewa game da masana'antar hakar ma'adanai har ya samu damar koyan dabarbarun kasuwanci daga mahaifinsa wanda hakan ya gyara masa hanya.

Kara karanta wannan

Kudin Da Aka Sace Karkashin Buhari Idan Aka Rabawa Yan Najeriya Kowa Zai Samu N700,000

A yanzu shekararsa 60, sannan ya narka hannun jari a bangaren wasanni, wanda yafi karfi a fannin kwallon kafa.

Har ila yau, shine yafi kowa hannun jari da kashi 37 a Pretoria-based Bulls, wanda a yanzu shine kungiyar rugby da take kan gaba a kasar Afirka ta Kudu.

BUA yayi fintinkau, ana tafka asara shi karuwa arzikinsa yake

A wani labari na daban, Abdussamad Rabiu, mamallakin kamfanin BUA ya samu karuwar arziki mai tarin yawa a shekarar 2022.

Duk da asarar da wasu masu arziki ke tafkawa, shi sai dai yayi hamdalah kan arzikin da ya samu a 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel