"Ba Bukatar Bulo": Wani Mutum Ya Gina Gangariyar Gida Da Kwantena 11, Kyawawan Hotunan Sun Burge Mutane
- Wani hazikin mutum ya nuna cewa ana iya yin wasu abubuwa da kwantena baya ga daukan kayayyaki masu nauyi
- Mutumin ya gina gida da manyan kwantenoni 11 ya kuma kawata cikin gidan da kayayyakin daki da lantarki
- Hotunan kyakyawan gidan sun bazu a kafafen sada zumunta inda mutane suka rika bayyana mabanbantan ra'ayoyi
Hotunan wani gida da aka gina shi da kwantenoni 11 ya janyo maganganu a shafukan sada zumunta na intanet.
Wani mai amfani da intanet MBM ya wallafa hotunan a wani shafi na Tell it All a Facebook inda ya ke bayyana sha'awansa ga gidan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa an kawata gidan da kayayyakin daki. Hotunan sun nuna gida da wani haziki mutum ya gina.
An jera kwantenoni kan junansu ta yadda suka yi tamkar gida mai bene a kan kasa.
A cikin gidan akwai kayan daki da aka saba gani a gidaje da lantarki da kayan girki. An kuma gano cewa gidan na da dakuna daban-daban sannan akwai lantarki.
Masu amfani da intanet sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan gidan
Ra'ayoyin masu amfani da soshiyal midiya
Jalil Akari ya ce:
"Wannan idan ka yi kuskure wani wayan lantarki ya taba kasa."
Naa Mina ya ce:
"Ba bukatar siminti da bulo."
Gaby F Monster ya ce:
"Kwantena 11 sun yi yawa wurin gina gida.
"Na san wani dan Najeriya da zai iya gina gida mai kyau da kwantena 5 kawai."
Kwabena Aboagaye Anyan ya ce:
"A gidan mu za su iya amfani da iskokai su daga kwantenan, sauran za su bi sahu."
James Agrah ya ce:
"Shin wannan ya fi saukin kashe kudi? Nawa ne kwantena mai tsawon kafa 20 ko 40? Shekaru nawa kwantenan zai yi kafin ya lalace?"
Nana Kwesi Boateng ya ce:
"Gidan da na ke kauna a rayuwa.
"Allah ka taimake ni.
"Idan ka gaji da unguwar, kawai wani filin za ka nema da tirela kawai sai ka yi gaba abin ka."
Eric Appiah ya ce:
"ET-Pablo Page bai da matsala idan an yi shi yadda ya dace. Ana yin irinsa sosai a kasashen Scandinavia."
Hotunan matashi dan shekara 16 da ya siyo daleliyar mota mai tsada
Wani matashi, Gift Salanje ya janyo musayar maganganu a dandalin Facebook bayan ya taya kaninsa dan shekara 16 murnar siyan sabuwar mota.
A wallafarsa, Gift ya saka hoton kaninsa a kan motarsa yana mai cewa yana alfahari da shi.
Asali: Legit.ng