Bayan Ba Turawa Mamaki a Gasar ‘World Cup’, Qatar Na Neman Karbar Bakuncin Gasar Olympics a 2036

Bayan Ba Turawa Mamaki a Gasar ‘World Cup’, Qatar Na Neman Karbar Bakuncin Gasar Olympics a 2036

  • Kasar Qatar ta aike da wani sako mai daukar hankali, tana kaunar karbar bakuncin wasannin Olympic na 2036
  • Kasashen India da Indonesia sun bayyana bukatar wannan dama, ga kuma Qatar ta sake bijiro da nata bukatar
  • Qatar ta sha mika bukatar karbar bakuncin wasannin, amma kwamitin shirya wasannin na duniya ya sha kin amincewa

Qatar - Gwamnatin kasar Qatar ta bayyana aniyar karbar bakuncin wasannin motsa jiki na Olympics da za a gudanar a shekarar 2036.

Wannan bayyana sha'awa a Qatar na fitowa ne daga kwamitin kula da harkokin motsa jiki na kasar, kamar yadda aka wallafa a shafin Twitter.

Kwamitin ya ce ya mika bukatar ne ta farko ga kwamitin shiya wasannin Olympica ta duniya don amincewa da bukatar Qasar, rahoton Marca.

Qatar na kaunar karbar bakuncin wasannin Olympic
Bayan Ba Turawa Mamaki a Gasar ‘World Cup’, Qatar Na Neman Karbar Bakuncin Gasar Olympics a 2036 | Hoto: eurosport.com
Asali: UGC

Wannan zai ba kwamitin na duniya duba yiwuwar ba Qatar dama ko hana ta karbar bakuncin wasannin da za a gudanar nan da shekaru kusan 12 masu zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

India da Indonesia na neman irin wannan dama

A bangare gudan kasashen nahiyar Asia; India da Indonesia sun bayyana sha'awar karbar bakuncin wasannin na Olympic da za agudanar, BBC Hausa ta ruwaito.

Gasar da aka kammala ta cin kofin duniya ta zo wa da kasar Qatar da alherai da yawa ta kudaden shiga, a tun farko kasar ta yi hasashen samun akalla dala biliyan 20 bayan kammala wasanni.

Hangen irin wannan ribar ne ta sa kasar ta Qatar ke kara sha'awar karbar bakuncin wasan duniya; a wannan karon wasannin motsa jiki na Olympic.

Ba wannan ne karon farko da Qatar ta fara neman karbar bakuncin wasan Olympic ba, a shekarun 2016, 2020 da 2032 ta nemi irin wannan bukata, amma kwamitin ya ki amincewa.

Mun haramta zina da shan giya a filin wasa - Qatar a wasan 'World Cup' 2022

Kasar Qatar ta jawo cece-kuce a duniya yayin da ta bayyana wasu ka'idoji da dokokin da take neman a kiyaye yayin gudanar da wasannin 'World Cup' da aka gudanar.

Kasar ta ce ta haramta shan giya da zinace-zinace hadi da kudurin hukunta 'yan luwadi da madigo da aka kama a lokutan wasannin.

Wannan yasa hukumomi da daidaikun jama'a a duniya ke ta yiwa kasar kallon mai take hakkin jama'a a wasannin da aka gudanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.