Al'adar Auren Korea Inda Ake Daure Kafar Ango a Lakada Masa Duka

Al'adar Auren Korea Inda Ake Daure Kafar Ango a Lakada Masa Duka

  • Yayin da kowacce al'ada take da yadda take bikin taya murnar aure, wasu na bada mamaki, wasu na tsoro, wasu na ban dariya
  • A kudancin Korea, matasan gari da 'yan uwan amarya suna daure kafafun ango sama hannaye a kafa gami da dukan kafarsa da tsumagiya
  • Kamar yadda suka yi imani cewa, hakan ne zai sa ya rike matar da kima, wanda iya yawan mutanen dake dukan angon iya darajar gidajen ma'auratan

Wurare da dama a fadin duniya suna da al'adun bikin aure mabambanta, wasu na bada tsoro, wasu su kan jawo cece-kuce, inda wasu keda ban mamaki ko ban al'ajabi.

Ango ake zanewa
Al'adar Auren Korea Inda Ake Daure Kafar Ango a Lakada Masa Duka. Hoto daga pulse.ng
Asali: UGC

Wata al'adar aure a kudancin Korea ta bar mutane da dama baki bude, inda aka ga ana daure tafin kafar ango gami da zane masa kafafu da bulala.

Kara karanta wannan

Jihohi 15 Da Za'a Iya Samun Rikici A Zaben 2023, Binciken Masana

Yayin da ake tunanin hakan kamar azabtarwa ne, al'adar ita kanta tana da kayatarwa da bakin da suka halarci bikin auren, sannan akwai wasu darussa da ke tafe da hakan, jaridar Pulse ta rahoto.

Game da wannan al'adar ta Kudancin Korea, wacce za a iya gani a matsayin wata al'adar wucin-gadi, matasan kauyen da 'yan uwan amaryar su kan shirya tarko daban-daban ga angon a gidan iyayen amaryar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wacce aka fi sani ita ce wacce matasa da 'yan uwan suke ratayewa angon kafafuwa a sama hannaye a kasa.

Sannan akwai lokacin da zasu yi amfani da farin kyalle su daure kafafunsa gami da fara dukan tafin kafarsa da abubuwa irinsu tsumagiya.

A lokacin da hakan ke faruwa, amaryar na rokon masu dukan da su dakata. Duk da basa sauraronta na wani lokaci.

Kara karanta wannan

Jami'an Rundunar Tsaron Farin Kaya DSS, Sunyi Gaba Da Babban Dalibin Abdul-Jabbar Sabida Sabawa Dokar Zaman Kotu

Yayin dukan, ana tambayar angon wasu tambayoyi wadanda ake sa ran ya amsa.

Ana cigaba da dukan, mahaifiyar amaryar na shirya abinci da abubuwan sha don rabawa ga abokan angon da sauran baki.

Bakin yayin ci da sha, suna karfafa masu dukan don cigaba da jibgar angon, wanda a ganinsu ita ce hanya mafi sauki da zai zama na kwarai.

Ana tsaka da haka, 'yan uwa da sauran mutanen kauyen zasu fara sanya wa ma'auratan albarka, wasu kuma su yi addu'ar tabbar farin ciki da lafiya ga ma'aikatan.

Sai dai, akwai yanayin da ba kowa bane yake bada gudunmawar a wannan al'adar, musamman idan ma'auratan ko 'yan uwansu suna da tarihi mara dadi ko basa girmama mutane.

Alamu sun tabbatar da cewa, iya yawan mutanen dake dukan angon, iya darajar gidajen ma'auratan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng