Jerin Shugabanin Kasashen Duniya Da Suka Fi Tsofa a Kafin Sauka Mulki

Jerin Shugabanin Kasashen Duniya Da Suka Fi Tsofa a Kafin Sauka Mulki

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya cika shekaru 80 cif a duniya ranar Asabar 17 ga watan Disamba, 2022, ana ganin yana cikin shugabannin da suka fi tsufa lokacin suna kan mulki.

Aminiya Hausa ta tattaro cewa a halin yanzun shugaba Buhari, wanda aka zaɓa ya hau karagar mulki a 2015, ya zama shugaban kasa ma fi tsufa a kan kujera lamba ɗaya a Najeriya.

Robert Mogabe.
Jerin Shugabanin Kasashen Duniya Da Suka Fi Tsofa a Kafin Sauka Mulki Hoto: aminiya
Asali: UGC

Sakamakon haka ne Legit.ng ta haɗa muku shugabanni biyar waɗanda suka fi tsufa a zamanin mulkinsu a wasu ƙasahen duniya.

1. Tsohon shugaban ƙasar Malawi, Hasting Banda

Hastings Banda, shi ne shugaban kasa na farko a ƙasar Malawi, ya gama wa'adin mulkinsa yana da shekaru 96. An haife shi a 1898 kuma ya yi mulki na shawon shekara 27.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Jiha Wuta, Sun Tafka Ɓarna

Banda ya sauka daga kan kujerar mulki a 1994 yana da shekaru 96 kuma ya kwanta dama a 1997.

2. Robert Mogabe na kasar Zimbabwi

Mogabe wanda ya sauka daga kujerar shugaban kasan Zimbabwe a 2017 yana da shekaru 93 a duniya ya rasu a shekarar 2019.

Ya kasance shugaban kasa ma fi daɗewa a tarin ƙasar Zimbabwe kuma saukarsa daga mulki ta zo cikin ruɗani.

Wasu bayanai sun nuna cewa juyin mulki aka masa amma Kotun Ƙoli tace shi da kansa ya yi murabus.

3. Beji Caid Essebsi na ƙasar Tunusiya

Shugaba Beji Caid Essebsi (1926–2019) na ƙasar Tunusiya ya jagoranci ƙasar daga 2014 zuwa lokacin rasuwarsa a 2019 yana mai shekaru 92 da watanni 9 a duniya.

Essebsi, wanda ya yi murabus daga matsayin Firaminista a shekarar 2011 bayan guguwar sauyi da kuma zaɓen da aka gudanar.

4. Shimon Peres na Isra'ila

Shimon Peres, tsohon shugaban Isra'ila na Tara a tarihi daga 2007 zuwa 2014 ya gama mulki yana da shekara 90 da watanni 11.

Kara karanta wannan

Mulki har sau 2: Jonathan ya aike da wani muhimmin sako mai daukar hankali ga Buhari

Peres (1923-2016), ya rike mukamain Firaminista sau biyu da Ministan harkokin waje sau uku, lokacin da ya sauka daga mulki a matsayin shugaba ma fi tsufa a duniya.

5. Joaquin Balaguer na Dominican

Tsohon Shugaban Kasar Jamhuriyar Dominican, Joaquin Balaguer, ya yi mulki karo biyu kuma a lokuta daban-daban (1960-1962 da kuma 1986-1996).

Ya sauka daga mulki yana da shekaru 89 da wata 11 a shekarar a 1996. Dukkanin waɗan nan da muka tattara muku sun girmi shugaba Buhari a zamanin da suke kan Mulki.

A wani labarin kuma Gwamnonin ci gaba na jam'iyyar APC sun taya shugaban ƙasa Buhari murnar cika shekara 80 a duniya ranar Asabar.

Gwamnonin APC sun tama Buhari murnar cika shekaru 80 a duniya, sun ce salon mulkinsa ka ƙayatar da 'yan Najeriya. Gwamnonin ta bakin Atiku Bagudu, sun faɗa wa shugaban irin tanadin da suke wa Bola Tinibu da sauran yan takarar APC a 2023.

Kara karanta wannan

Darusa 10 da Za a Dauka daga Shari’ar Sheikh Abduljabbar Kabara – Kabir Asgar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262