Hamshakin Mai Kudi ya Siya Tsohon Wandon da Aka Tsamo a Kasan Teku kan N50m
- Wani mutumi ya lale makuden kudi har N50.78 miliyan ya siya wani wandon jins din da aka zakulo a kasn teku
- Mutum na karshe da ya saka shi jirgi ya nitse dashi shekaru 165 da suka gabata kuma babu tabbacin ko wanda ya siya zai iya sakawa
- Wandon baturen mai hako ma’adanan ya samu masu siyansa da tarin yawa bayan an fitar da gwanjonsa a Amurka
Wani wandon maza wanda aka gano ya kasance mafi tsufa da dadewa an yi gwanjonsa kan $114,000 wanda yayi daidai da N50.7 miliyan.
BBC ta rahoto cewa, farin wandon an tsamo shi ne daga wani jirgin ruwa da ya nitse tun a shekarar 1857 a Arewacin Carolina.
A yayin jawabi kan nasarar da aka samu wurin siyar da shi, Dake Dwight Manley, manajan California Gold Marketing Group yace:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Wannan wandon mai hako ma’adanan tamkar tutar farko suke, sun kafa tarihi. Babu irinsu yanzu kwata-kwata a duniya.”
Bayani kan jirgin ruwan
Jirgin ruwan ya nitse a watan Satumban 1857 inda mutum 425 suka mutu daga cikin fasinjoji 578 da matukan da ya dauko.
Fasinjojin na dauke da tan 21 na sulalla da gumaka yayin da jirgin ruwan ya nitse. An gano hakan ne a karo ba farko a shekarar 1988.
Waye ya siya wandon?
Wani mutumi daga Oregon, wanda ya siye su a San Francisco ne ya zuba Kudi ya kwashe, cewar kamfanin gwanjon.
Jami’an gwanjon sun ce wandon mai botura biyar ya nuna kirkira ta farko da Levi Strauss suka fara siyarwa na kaya a karni na 17, jaridar Guardian ta rahoto.
Jama’a sun yi martani
@Darius Nawrock7 ya rubuta:
Bidiyo: Kare Ya Kama Uwar Gidansa Na Jin Daɗi da Saurayi a Ɗaki, Ya Bankaɗe Mutumin Ya Maye Gurbinsa
“Toh, yanzu dai mun san yayin da za a yi shekara mai zuwa.”
@stevedw82 ya kara da cewa:
“Ina fatan wanda ya siya zai saka a jikinsa.”
@Vallabh Sonawane yace:
“Zan ba ka irin wannan wandon sak kan $2.”
Mashahurin mai arziki ya gina gidaje 90, ya Kyautar dasu
A wani labari na daban, wani hamshakin mai arziki ya tamfatsa ginin gidaje 90 masu iri daya.
Sai dai ya Kyautar dasu ga masu bukat duk don murnar auren diyarsa.
Asali: Legit.ng