Tsohuwa mai Shekaru 90 ta Kammala Digiri Bayan Shekaru 71 da Shiga Jami’a
- Tsohuwa mai shekaru 90 mai suna Joyce DeFauw ta kammala digirinta na farko daga jami'a bayan kwashe shekaru 71 da shiga
- A ranar Lahadi tsohuwar mai yara 9 ta samu digirinta na farko a jami'ar Arewacin Illinois bayan ta shiga a shekarar 1951
- Ta sanar da cewa lamurra ne suka sha gabanta, hakan yasa tayi aure har sau biyu kuma ta haifa yara 9 wanda daga bisani suka sa taje ta karasa karatun
Amurka - Wata kaka mai shekaru 90 a duniya ta kammala karatu a jami’ar Arewacin Illinois dake kasar Amurka a ranar Lahadi, jaridar Punch ta rahoto.
Joyce DeFauw ta karba kwalin digirinta na farko bayan shekaru 71 da tayi tana karatu a jami’ar.
Tana daya daga cikin masu shekaru mai yawa da suka taba kammala digiri a jami’ar.
“Akwai abubuwa da yawa dake gabana da suka sa bana iya fahimtar komai.”
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
- DeFauw tace.
Yaushe ta shiga jami'ar?
Ta shiga jami’ar a 1951 a lokacin da take Kwalejin Malamai ta Arewacin Illinois.
DeFauw ta fara karantar Early Elementary major, sai Home Economics daga nan sai German, Typing da Bookkeeping.
Soyayya ta ja ta
Sai dai, ta fada soyayya sannan ta jingine karatu a gefe.
Tace ta tuna:
“Wayyo Allah, a cocinmu akwai wani matashi da ya kasance hadadde. A bayyane yake shi ma ya ga haduwata. Sai muka yanke hukuncin kasancewa tare kuma na yanke hukuncin barin makarantar.”
Mijinta ya mutu ta kara aure
Jaridar The Nation ta rahoto cewa, mijinta ya mutu kuma ta sake aure. A jimilla tana da yara tara amma ba ta manta da makaranta ba.
Tace:
“Yarana sun ce sun so da na fada musu. Da na kammala karatun. Kuma sun yi tunani da shawarar me zai sa ba zaki koma yanzu ba? Ba ki da abun yi. Nayi tunanin gaskiya suka fadi. Sai na yanke hukuncin komawa. Amma ina bukatar kwamfuyuta.”
Sun siya min daya a 2019 kuma na koma makaranta.
Ta kammala karatun
Ta kammala dukkan karatun ta a yanar gizo inda take rayuwa a Geneseo dake Illinois.
“Toh, an bani ajujuwa amma akwai lokutan da naso watsi da karatun.”
- DeFauw tace.
“Amma na ji dadi da ban bari ba. Sun ce kada ki bari saboda kin kusa. Kada ki sare yanzu. Kuma gashi nan ina godiya da ban bari ba.”
An dauka nauyin kammala karatun ta kuma makarantar tana bayyana ta matsayin wata madubin dubawa tare da cewa sun koyi darussa daga wurinta.
A yayin karawa wasu kwarin guiwa, tace lokaci bai kure maka ba na kammala karatu.
Ta kara da cewa:
“Akwai abubuwa da yawa da za ka koya kuma rayuwa tana da ban sha’awa kuma kowannenmu yana da baiwarsa. Duk muna nan ne saboda dalili.”
Tsohon ministan Buhari ya kammala karatu
A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin Najeriya, Chibuike Amaechi, ya kammala karatu a jami'ar Baze.
Fitaccen 'dan siyasan ya kammala digiri a fannin shari'a.
Asali: Legit.ng