Kamfanin Meta, Mamallakin Facebook Sun Fatattaki Sama da Ma’aikata 11,000
- Shahararren kamfanin Meta wanda su ke da dandalin sada zumuntar zamani ta Facebook, sun sallami sama da ma’aikatansu 11,000
- Kamar yadda aka gano, hakan na wakiltar kashi 13 na jimillar dukkan ma’aikatan kamfanin kenan da suka rasa ayyukansu
- Mark Zuckerberg, mamallakin kamfanin ne ya sanar da ma’aikatansa a wani sako da ya aike dakin labaran kamfanin Meta din
Meta, kamfanin manhajar dandalin sada zumuntar zamani na Facebook ya sallami sama da ma’aikatansa 11,000 wanda hakan ke wakiltar kashi 13 na dukkan ma’aikatan kamfanin, The Cable ta rahoto.
Mark Zuckerberg, mamallakin kamfanin ya sanar da hakan a sakon korar aiki ga ma’aikatan wanda Meta ta tura dakin labaranta, Channels TV ta rahoto.
Jawabin Zuckerberg
Ya bayyana cewa kamfanin na shirin rage kudaden da yake kashewa tare da dakatar da daukar ma’aikata har zuwa wata ukun farkon shekara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“A yau ina sanar da ku sauyi masu wahala da muka yi a tarihin Meta. Na yanke hukuncin rage yawan tawagarmu da kashi 13 kuma mu bar sama da zakakuran ma’aikatanmu 11,000 su tafi.
“Za mu sake daukan wasu matakan rage yawa da kuma aikin kamfanin yadda ya dace ta hanyar rage kudin kashewa da dakatar da daukar ma’aikata zuwa wata ukun farko na shekara mai zuwa.”
- Zuckerberg yace.
“Ina son daukar alhakin wannan hukuncin da kuma yadda muka tsinci kanmu a nan. Ina matukar nada hakuri ga wadanda abun ya shafa.”
- Ya kara da cewa.
Dalilin daukar matakin rage ma’aikata
Zuckerberg yace wannan cigaban ya biyo bayan hukuncin kara hannayen jari a farkon annobar korona. Sai dai cike da takaici hakan bai haifar da abinda ake tsammani ba.
Ya bayyana cewa wadanda lamarin ya shafa a Amurka zasu samu kudin sallama na makonni 16 tare da karin na makonni biyu a kowacce shekarar aiki.
Wadanda ke wajen Amurka kamar yadda Zuckerberg yace zasu samu makamancin hakan kuma kamfanin zai bi tsarikan dokokin kasarsu.
Kamfanin ya sauya suna a cikin shekarar nan daga Facebook zuwa Meta wanda har yanzu jama’a basu saba da sabon sunan ba.
Tuni aka saba da sunan Facebook wanda shi ne dandalin sada zumuntar zamanin da jama’a suka fi sabawa da shi.
Asali: Legit.ng