Amou Haji: Mutumin da yafi kowa kazanta a duniya, ya yi shekaru 67 babu wanka, yana kwana a rami

Amou Haji: Mutumin da yafi kowa kazanta a duniya, ya yi shekaru 67 babu wanka, yana kwana a rami

  • Amou Haji tsoho ne mai shekaru 87 dan kasar Iran wanda ya kwashe shekaru 67 bai yi wanka ba
  • An gano cewa tsohon yana matukar tsoron ruwa kuma bai sake wanka ba tun yana saurayi, kusan kwanaki 25,000
  • Duk da Amou baya wanka, yana shan a kalla lita biyar ta ruwa daga wani gwangwani mai tsatsa a kowacce rana

Iran - Amou Haji tsoho ne mai shekaru 87 wanda ya kwashe shekaru 67 bai yi wanka ba. Tabbas hakan yake.

Tsohon dan asalin kasar Iran yana rayuwarsa ne kusa da wani kauye dake kusa da yankin Kermanshah shi kadai kuma ya yi a kalla shekaru 67 babu wanka.

Amou Haji: Mutumin da yafi kowa kazanta a duniya, ya yi shekaru 67 babu wanka, yana kwana a rami
Amou Haji: Mutumin da yafi kowa kazanta a duniya, ya yi shekaru 67 babu wanka, yana kwana a rami. Hoto daga Indiatimes.com
Asali: UGC

Yanayin rayuwar Haji

Kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar,, Haji a kodayaushe za ka gan shi lullube da toka da datti kuma baya wanka saboda tsoron ruwa da yake yi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Kada Ku Zabi Duk Wanda Yace Abubuwa Zasu Yi Sauki, Sanusi Ga Yan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon mai shekaru 87 ya yadda cewa idan har yayi wanka, toh babu shakka zai iya faduwa mugun ciwo.

Abincin da tsohon yake ci sun hada da rubabben nama da matattun dabbobi. Yana matukar jin dadin cin bushiya da shan tabarsa ta koko, India Times ta ruwaito hakan.

A wasu lokutan kuwa, Haji yana busa hayakin kashin dabbobi a kokon tabarsa.

Killataccen tsohon ya yanke shawarar irin wannan sabuwar rayuwar ne bayan da ya samu wani babban kalubale a zamanin samartakarsa.

Duk da tsohon bai yarda da yin wanka da ruwa ba, an gano cewa yana shan a kalla lita biyar ta ruwa a kowacce rana daga wani gwangwaninsa mai tsatsa, Times Now News ta ruwaito.

Yana gyara gashin kansa ne tare da rage masa tsawo ta hanyar kona shi da wuta.

Kara karanta wannan

Muna Shawaran Sake Ciwo Bashi Daga Wajen Asusun Lamunin Duniya, Ministar Kudi

Sai mun kakkabo ragowar 'yan ta'addan dake yankin tafkin Chadi, MNJTF

A wani labari na daban, Manjo janar Abdul-Khalifah Ibrahim, kwamandan sojojin MNJTF ya bukaci rundunonin soji da su shirya ragargazar ragowar mayakan Boko Haram da suke wuraren tafkin Chadi.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a wata takarda ta ranar Juma’a, Shugaban fannin yada labaran soji na MNJTF, Kanal Muhammad Dole ya ce Ibrahim yayi wannan maganar ne a lokacin da ya zagaya sansanonin sojojin yankin.

Dole ya ce a makon da ya gabata kwamandan ya kai ziyara bangare na uku dake Monguno a Najeriya, bangare na daya dake Moura a Kamaru da bangare na boyu dake Bagasola a Chadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel