Kofur Oliveira: Kare Jami’in ‘Dan Sanda dake Cakarewa da Gilashi Har da Bindiga

Kofur Oliveira: Kare Jami’in ‘Dan Sanda dake Cakarewa da Gilashi Har da Bindiga

  • Kofur Oliveira fitaccen kare ne wanda ya kasance jami’in ‘dan sandan da ya shahara a kafafen sada zumuntar zamani
  • Ubangidan karen mai suna Cristiano ‘dan sanda ne da ya tsinta karen da rauni, a gajiye kuma yana jin yunwa amma ya gyara shi tare da horar da shi
  • Kofur Oliveira a halin yanzu yana da mabiya 120,000 a Instagram kuma a yanzu jami’i ne a bataliya ta 17 na ‘yan sandan Rio de Janeiro dake Brazil

Brazil - Wani shahararren karen ‘yan sanda yayi suna kuma ya zama abun nuni a Brazil bayan shuhurar da yayi a kafafen sada zumuntar zamani.

Kofur Oliveira na Brazil
Kofur Oliveira: Kare Jami’in ‘Dan Sanda dake Cakarewa da Gilashi Har da Bindiga. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

Cristiano Oliveira, wani jami’in ‘dan sanda a Rio de Janeiro, ya tsinta karen kusa da ofishin ‘yan sanda kusan shekaru uku da suka gabata, jaridar TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: Yadda na Biya Cin Hanci Wajen Shigo da Hodar Iblis Inji Shaida a Kotu

Kamar yadda Reuters ta bayyana, jami’in ‘dan sandan ya ga karen an yi watsi da shi, dauke da rauni a kuma yunwace.

A yadda aka tsananta horar da karen, Kofur Oliveira ya zama fitacce a soshiyal midiya a Brazil.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A halin yanzu, karen ya kasance jami’in ‘dan sandan Rio de Janeiro a bataliya ta 17 wadanda suke sintiri tare da Cristiano yayin suke kan babura.

A matsayinsa na jami’in ‘dan sanda, Kofur Oliveira a koyaushe ana ganinsa sanye da kayan ‘yan sanda da bindigar wasa sanye da gilashi.

A kan yadda ya shahara a kafafen sada zumunta, Cristiano yace:

“Na dauka rigar sama, rigar ‘yan sanda kuma na saka masa a matsayin wasa. Na dauka hotonsa kuma na tura guruf din ofisoshin ‘yan sanda inda suma suka dinga wallafawa. Daga nan ne wasan ya bazu.”
“Idan ban saka hotonsa ba ba tsawon kwanaki uku, jama’a sai su dinga tambayar ina Oliveira? Ina Oliveira ya je?”

Kara karanta wannan

Yadda Aka Yi Rabon Biredi A Wajen Wani Kasaitaccen Biki Na Gani Na Fada, Bidiyon Ya Ja Hankali

Karen yana da shafinsa na Instagram inda yake da mabiya sama da 120,000.

Har Masu Zundena Kan Kwasar Bola da Nake yi Sun bi Sahu na: Tsohuwa Mai Shekaru 63

A wani labari na daban, Amdalat Taiwo Pedro mata ce da mijinta ya mutu amma take sana’ar kwashe bola a titinan Legas a kokarinta na samun abinda zata ci da kuma kula da kanta.

Sakamakon hauhawar farashi da tsananta rayuwa a kasar, mutane da yawa sun kama sana’o’i wadanda a baya ba zasu taba yin su ba, BBC News ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng