Sharrin Boka: Wata Budurwa Ta Kashe Mahaifiyar Saurayinta Ana Shirin Aure

Sharrin Boka: Wata Budurwa Ta Kashe Mahaifiyar Saurayinta Ana Shirin Aure

  • Wata matashiyar budurwa mai suna Mabel, ta ɗauki shawarar wani Boka ta hallaka mahaifiyar saurayin da zata aura
  • Rahotanni sun nuna cewa budurwar ta garzaya wurin Bokan ne da nufin ya neman mafita kan rashin baccin dare, sai ya bata wannan shawara
  • Tuni dai jami'an tsaro suka cafke ta kuma bincike ya gano tana ɗauke da ciki na watanni biyar

Wani rahoto daga ƙasar Kamaru ya nuna cewa hukumomi sun kama wata budurwa bisa zargin kashe mahaifiyar saurayinta. An ce lamarin ya auku ne ranar Litinin a Fongo-Ndeng.

BBC Hausa ta ruwaito cewa matashiyar budurwar mai suna, Mabel, ta yi amfani da adda ta sare kan matar 'yar kimanun shekara 64, wacce take uwa ga wanda zata aura.

Taswirar ƙasar Kamaru.
Sharrin Boka: Wata Budurwa Ta Kashe Mahaifiyar Saurayinta Ana Shirin Aure Hoto: punchng

Wasu bayanai sun tabbatar da cewa Mamaciyar ce ke kokarin nema wa ɗanta auren budurwar, inda gabanin a kammala shirye-shirye, ta kaita gidanta suna rayuwa tare.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da miji ya kai karar matarsa saboda ya sake ta amma ta ki barin gidansa

Meyasa Budurwar ta aikata wannan ɗanyen aiki?

Bayan koma wa gidan surukarta da zama, Mabel, ta yi ikirarin cewa ba ta samun bacci da daddare, bisa haka ta garzaya wurin wani Boka domin ya bata magani.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu rahotanni sun ce bayan ta zayyana wa Bokan matsalarta, ya gaya mata cewa abinda ke faruwa da ita alamu ne na maita. Bokan ya kuma shawarce ta kan ta kashe Surukarta.

Daga nan, budurwar bata ɓata lokaci ba ta kashe surukarta mai suna, Ma'a Cecilia, da tsakar dare yayin da take bacci. Daga bisani kuma ta yi amfani da Adda ta cire wuyan mamaciyar.

An ce matashiyar ba ta tsaya iya nan ba, sai da ta yi gunduwa-gunduwa da sassan jikin Surukarta. Tuni dai jami'an tsaro a Kamaru suka yi ram da ita.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa jami'an tsaro na tuhumar budurwa da ajalin Surukarta. A wani ɓangaren kuma bincike ya tabbatar da tana ɗauke da ciki na wata biyar.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar da Gwamna Wike Sun Amince da Bukata Ɗaya Kafin Fara Kamfen 2023

A wani labarin kuma Wata Matar Aure ta shaida wa Kotu musabbabin da ya sa take hana mijinta damar kwancuyar aure da ita

Matar ta kai karar mijin gaban Kotun kostumare da ke Ibadan, jihar Oyo ne saboda tace tana rayuwar baƙin ciki da 'ya'yanta.

Bayan sauraron kowane ɓangare, Alƙalin Kotun ya ɗage sauraron karar zuwa ranar 30 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262