Tirkashi: Yadda Matukan Jirgi Biyu Suka Ba Hammata Iska Ana Tsaka Da Tafiya A Sama, Sai Da Aka Shiga Tsakani

Tirkashi: Yadda Matukan Jirgi Biyu Suka Ba Hammata Iska Ana Tsaka Da Tafiya A Sama, Sai Da Aka Shiga Tsakani

  • Wasu matukan jirgin sama biyu sun ba hammata iska yayin da suke jigilar mutane daga Geneva zuwa Faris
  • Jim kadan bayan jirgin ya fara shawagi a sama sai aka samu rashin fahimta a tsakaninsu inda daya ya fallawa daya mari, sai suka ci kwalar rigunan juna
  • An sauka lafiya bayan sauran ma'aikatan jirgin da suka firgita sun shiga tsakaninsu tare da tabbatar da fadan bai ci gaba ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Faransa - An dakatar da wasu matukan jirgi guda biyu bayan sun jefa rayuka cikin hatsari lokacin da suka fara dambe da junansu jim kadan bayan jirgin da suke tukawa ya tashi sama.

Fada ya barke a tsakanin ma’aikatan jirgin saman na Air France bayan daya daga cikinsu ya ki bin umurni kan tashin jirgin daga Geneva zuwa Faris, jaridar Daily Mirror ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ya Guje Mu Saboda Baya Son Tagwaye: Bidiyon Sauyawar Wata Mata Da Yan Biyunta Ya Ba Da Mamaki

Sai matukin jirgi daya ya mari dan uwansa, kafin suka ci kwalar rigar junansu.

Jirgin sama
Tirkashi: Yadda Matukan Jirgi Biyu Suka Ba Hammata Iska Ana Tsaka Da Tafiya A Sama, Sai Da Aka Shiga Tsakani Hoto: The Independent
Asali: UGC

Daya daga cikin matukan jirgin ya jefi dayan da akwati a fuska, a wannan matakin ne, ma’aikatan jirgin da suka cika da tsoro bayan jin abun da ke faruwa a bangaren matukan suka shiga ciki suka raba su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shafin LIB ya rahoto cewa wani ma’aikacin jirgin da ya raba dambe ya shafe sauran lokacinsa ne wajen zaman zuba idanu kan matukan jiragen don hana su sake dambatuwa a tsakaninsu.

Matukan jirgin suna kan aikin jigala daga Geneva zuwa Faris a watan Yuni, kamar yadda wani jami’in kamfanin jirgin na Air France ya bayyana a ranar Lahadi, 28 ga watan Agusta.

Jirgin ya ci gaba da tafiya kuma sun sauka lafiya, kuma hargitsin bai shafi sauran tafiyar ba, in ji jami’in, yana mai cewa kamfanin jirgi ya jajirce wajen tabbatar da kare rayuka.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Wani ya yi aikin dana sani, ya kashe masoyiyarsa saboda katin ATM

Sabon Shiga: Bidiyon Yadda Matashi Ya Zunduma Ihu Cike Da Tsoro Bayan Ya Shiga Jirgin Sama A Karon Farko

A wani labarin, wani bidiyo mai ban dariya na wani matashi bakin fata da ya shiga jirgin sama a karon farko ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu.

A cikin bidiyon wanda ya yadu a soshiyal midiya, an gano matashin yana jan numfashi sannan ya kurma ihu yayin da jirgin saman ya lula iska.

Wani mutum da ya cika da mamaki ya zauna kusa dashi sannan ya nadi bidiyonsa yayin da yake dariya ba kakkautawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng