So Nake su Koyi Sana'a da Tattali: Mata Mai Gidan Gona ta ba Yaranta Aiki, Albashinsu 105k a Sati
- Wata matar aure a garin Kitengela ta sha jinjina da yabo a soshiyal midiya bayan ta bai wa yaranta maza masu shekaru shida da tara aikin yi
- Shawn mai shekaru shida zai dinga kwashe kwai daga gidan gonarta yayin da Ryan mai shekaru tara zai dinga baiwa shukoki ruwa a gonar
- Kimoi Jerotich ta sanar da kafar yada labaran Kenya cewa, ta yi hakan ne domin ta koyawa yaranta adani da tattali tun suna yara
Kimoi Jerotich, wata mata mai yara uku ta bai wa jama'a mamaki bayan wasikar daukar aikin da tayi wa yaranta biyu ta bayyana.
A wasikar da ta yadu a soshiyal midiya, Jerotich ta dauka Shawn mai shekaru shida da Ryan mai shekaru tara aikin shekaru uku kacal.
Shirin gaba nake musu
A yayin tattaunawa da kafar yada labaran Kenya ta Tuko.co.ke, HRM tayi bayanin cewa ta yanke wannan hukuncin ne saboda tana son shirya yaranta saboda gaba da wuri.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda tace, yaranta maza sun saba ayyukan gida amma ta kara musu da wannan ne saboda su fahimci cewa kudi samunsu ake yi.
"Ina son su gane cewa zamu iya samun kwanmu a nan gida ba tare da mun siya daga wasu manoma ba," tace.
Jerotich ta kara da cewa, a hakan da take yi tana kokarin ganin ta koyawa yaranta dabi'ar adani kuma sun yarje duk kudin da suka samu zasu dinga adanawa a banki ne.
Za a sabunta kwangila bayan shekaru uku
Abinda yafi daukar hankali a batun wannan kwangilar shine yadda tace za a sabunta ta bayan shekaru uku duba da kokarin da yaran suka yi.
"A cikin shekaru uku, wanda ke shekaru tara zai kai 12 kuma dayan zai kai shekaru tara, don haka hatta takardar kwangilar zata sauya," ta cigaba da cewa.
Kamar Almara: Kyakkyawar Budurwa Ta Wallafa Sakonnin Soyayya Da Mai Gadinta Ya Tura Mata Ta WhatsApp
Jerotich ta cigaba da bayyana abinda ta shirya kwanakin baya sai dai tace sun fara ne N70.29 sannan ta kara musu N35.14.
"Ba ku ga yadda suke farin ciki ba ranar da suka zo tunatar da ni cewa ranar biyansu albashi tayi," tace.
Za a bai wa auta aiki idan ta ka shekaru 5 a duniya
Abinda tafi lura da shi kamar yadda tace shine, matasan ba zasu gane me ake nufi da saka hannun jari ba amma wata rana takardun nan zasu zama masu amfani garesu.
Ganin cewa a matsayin HR take aiki, tana shirin rubutawa kowanne daga cikinsu takardun neman aiki ta yadda idan zasu je intabiyunsu ta farko ba zasu zama baki ba.
Tana fatan iyaye zasu koya wannan dabi'ar daga wurinta ta yadda kowannen iyali zasu tarbiyyantar da yara masu sanin ya kamata.
"Ta wannan hanyar, idan yarana suka auri diyar wasu nan gaba, kowannensu yana da sana'ar yi wanda yana da matukar kyau a gaba," tace.
Doguwar Mace: Bidiyoyin Magidanci Da Santaleliyar Matarsa Sun Haifar Da Cece-kuce, Iya Kugunta Ya Tsaya
Jerotich ta kara da bayyana cewa tana da yarinya mai shekaru biyu wacce zata bai wa aiki idan ta kai shekaru biyar.
Asali: Legit.ng