Bidiyo: Yadda Aka Tsarkake Ka'aba, Yariman Saudiyya Yayi Jagoranci
- Bidiyon yadda aka tsarkake Ka'aba na wannan shekarar wanda aka yi shagalin a ranar Talata da ta gabata ya bayyana
- Kamar yadda bidiyon ya nuna, Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman ne ya jagoranci wanke Ka'aba inda da hannuwansa ya wanke bangon ciki
- Ana amfani da ruwan Zamzam da turaren Miski inda ake jika fararen kyalle a ciki sannan a wanke cikin, kasan kuwa da hannu da ganye ake dirje shi
Saudi Arabia - Kamfanin Dillancin Labaran Saudi a ranar Talata ya rahoto yadda yariman kasar, Mohammed bin Salman ya jagoranci bikin wanke Ka'aba da ake yi kowacce shekara na Sarki Salman bin Abdulaziz.
Kamar yadda SPA ta bayyana, Yarima Abdulaziz bin Turki, ministan wasanni, ya raka shi inda Abdulrahman bin Abdulaziz al-Sudais, shugaban lamurran masallatai biyu, ya karbe shi.
A Twitter, SPA ta bayyana bidiyon yadda yarima mai jiran gadon yana wanke bangon cikin ka'aban da kyalle.
Ana yin wannan wankin ka'aban ne a kowacce shekara kamar yadda al'ada ta tanadar, jaridar The Islamic Information ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Akwai banbancin yadda bangon ka'aba da kasanta ake wankesu. Ana saka fararen kyallaye a ruwan turare da miski sannan a yi amfani da su wurin wanke bangwayen ciki, yayin da ake amfani da ruwan Zamzam da turare wurin wanke kasa inda ake takawa.
Ana amfani da hannuwa da kuma ganye wurin goge kasan da wannan ruwan Zamzam da turaren.
Kotun Saudiyya Ta Yankewa Daliba Hukuncin Shekaru 34 a Magarkama Kan Amfani da Twitter
A wani labari na daban, wata dalibar jami'ar Leeds mai suna Salma al-Shebab mai shekaru 34 wacce ta dawo daga Ingila bayan hutun da taje, ta shiga hannun hukuma kuma aka yanke mata hukuncin shekaru 34.
An yanke mata wannan hukuncin nan ne sakamakon amfani da asusunta na Twitter da kuma bibiya tare da sake wallafa maganganun masu rajin kare hakkin mata.
Mahaifiyar yara biyun ana zarginta da amfani da Twitter wurin tada tashin-tashina da tada tarzoma tare da karantsaye ga tsaron kasa bayan ta yi wallafa kan hakkin mata a Saudi Arabia.
Asali: Legit.ng