Mace Yar Shekara 64 Ta Lashe Zaben Shugaban Kasa a Indiya

Mace Yar Shekara 64 Ta Lashe Zaben Shugaban Kasa a Indiya

  • Droupadi Murmu, wata mata yar shekaru 64 ta zama shugaban kasa a Indiya bayan lashe zabe
  • Murmu, ita ce mace ta biyu a tarihin kasar da ta zama shugaban kasa, kuma ta fito ne daga kabilar Santhal mara rinjaye
  • Zababbiyar shugaban kasar ta fara aiki ne a matsayin malamar makaranta sannan daga bisani ta shiga siyasa ta rike mukamin minista da gwamna

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Indiya - An zabi wata mace, Droupadi Murmu, daga kabila mara rinjaye a matsayin shugaban kasar Indiya a ranar Alhamis bayan samun goyon bayan jam'iyya mai mulki, hakan yasa ta zama mutum na farko daga marasa rinjaye da ta rike mukamin.

Droupadi Murmu.
Mace Yar Shekara 64 Ta Lashe Zaben Shugaban Kasa a Indiya. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Murmu, wacce ta fito daga kabilar Santhal, ta samu mafi rinjayen kuri'u daga fiye da rabin yan majalisa da yan majalisar jihohi, kamar yadda wani sashi na sakamakon da aka fitar ya nuna.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Yadda wata ta yi digiri shekaru 4 bayan likitoci sun bata wa'adin mutuwa cikin watanni 12

Jam'iyya mai mulki na Hindu nationalist Bharatiya Janata Party, BJP ce ta zabi Murmu, mai shekaru 64 domin takarar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Modi ya wallafa rubutu a Twitter na taya Murmu murna yana cewa 'nasarar ta zai karfafawa dukkan yan Indiya gwiwa.'

'Nasarar ta ya zama abin karfafa gwiwa ga yan kasarmu, musamman talakawa, wadanda aka nuna wa wariya da marasa rinjaye'

Wanda ke biye da ita a zaben, Yashwant Sinha - tsohon mamba na BJP kuma tsohon ministan kudi da harkokin kasar waje shima ya taya ta murna.

Murmu ce za ta zama shugaban kasa mace na biyu a Indiya bayan Pratibha Patil, wacce ta rike mukamin na shekaru fiye da biyar daga 2007.

Takaitaccen tarihin Murmu

An haife ta ne a Mayurnhanj a gabashin Odisha, zababbiyar shugaban kasar ta fara aiki ne a matsayin malamar makaranta kafin ta shiga siyasa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnatin Buhari na duba yuwuwar haramta Okada a Najeriya

Ta rike mukamin minista a gwamnatin jiha kuma ta yi gwamna a jihar Jharkhand.

INEC ta bawa Ademola Adeleke takardar shaidar nasarar cin zaɓe

A bangare guda, hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta mika takardar shaidan nasarar cin zaɓe ga Ademola Adeleke, zabebben gwamnan Jihar Osun kuma ɗan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, rahoton The Cable.

Adeleke ya samu kuri'u 403,371 inda ya doke Gboyega Oyetola, gwamnan Osun kuma ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress APC a zaben na gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164