Hotunan ƙasaitaccen shagalin auren kwaɗi da aka shirya a India don roƙon ruwa, an yi ruwan sama washegari

Hotunan ƙasaitaccen shagalin auren kwaɗi da aka shirya a India don roƙon ruwa, an yi ruwan sama washegari

  • Wasu mutane a kasar Indiya sun shirya kasaitaccen shagalin bikin kwadi wanda suka kashe kudi kuma aka ci aka sha
  • An gano cewa, sun yi bikin ne domin rokon ruwan sama sakamakon tsananin fari da zafin da yankin Gorakhpur ke fuskanta
  • Sai dai cike da abun mamaki, washegarin yin wannan bikin don farantawa ubangijin ruwansu mai suna Indra, sun samu ruwan sama mai yawan gaske

Indiya - Wata kungiyar mutane a birnin Gorakhpur dake Indiya sun shirya kasaitccen bikin kwadi biyu domin kiran ruwa bayan watannin da suka kwashe suna fama da rashin ruwan sama wanda ya janyo tsananin zafi.

Kungiyar sun samu kwadi biyu a ranar 19 ga watan Yuli kuma sun yi bikin domin farantawa ubangijin ruwa Indra, rai.

Kwadi
Hotunan ƙasaitaccen shagalin auren kwaɗi da aka shirya a India don roƙon ruwa, an yi ruwan sama washegari. Hoto daga indianexpress.com
Asali: UGC

Indian Express sun rahoto cewa, sun tirsasa kwadin biyu auren juna a matsayin wani bangare na tsafin duk da kokarin da suka dinga na ganin amarya da angon tare.

Kara karanta wannan

Hotuna: Zukekiyar diyar Kashim Shettima, Fatima Shettima zata amarce, katin gayyata ya fito

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Biki ne da ake matukar kashe kudi kuma daruruwan mutane sun je kallon shagalin wanda ya hada da manyan limaman addinin gargajiya wadanda ke ta addu'o'i sannan suka cika tumbinsu bayan bikin.

Mashiryin bikin, Radhakant Verma yace: "An dade da sanin cewa ana auren kwadi ne domin kiran ruwan sama.
"Mun dade muna fuskantar fari kuma manomanmu sun fusata kan jinkirin shuka."

A sa'o'in farko na ranar 20 ga watan Yulin 2022, kwana daya bayan bikin kwadin, an yi ruwan sama mai tarin yawa ga sassan kasar har da Gorakhpur, Uttarakhand, Himachal Pradesh, Punjab, Haryana, Chandigarh, Delhi, Uttar Pradesh, West Madhya Pradesh, Arunachal Pradesh da Assam, Meghalaya.

Sashen kula da yanayi na kasar Indiya yace: "Ruwa mai tsananin yawa ya sauka a wasu wuraren dake fama da matsanancin zafi."

Kara karanta wannan

Yadda matashi ya sace janareto da lasifikar Masallaci a Adamawa, ya sheke kudin a tabar wiwi

Kwadi
Hotunan ƙasaitaccen shagalin auren kwaɗi da aka shirya a India don roƙon ruwa, an yi ruwan sama washegari. Hoto daga indianexpress.com
Asali: UGC

'Dan uwan ango ya bindige amarya ana tsaka da shagalin biki, ta sheka lahira

A wani labari na daban, ana tsaka da shagalin biki, an bindige amarya yayin da 'dan biki ya harba bindiga duk a cikin murna kuma ya sameta a kan ta.

Mahvash Leghaei mai shekaru 24 tayi aure a Firuzabad a Iran yayin da 'dan biki wanda ya kasance 'dan uwan ango ne, ya harba bindigarsa mara lasisi wacce yake amfani da ita wurin farauta.

An gano cewa, kai tsaye harsashin ya shiga kan mata kuma ya jigata 'yan biki maza har su biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng