Bidiyo: Baturiya da ta aura 'dan Najeriya tace tana jin dadi, ta shiga cikin matan kauye tana shara da wanki

Bidiyo: Baturiya da ta aura 'dan Najeriya tace tana jin dadi, ta shiga cikin matan kauye tana shara da wanki

  • Wata baturiya da ta auri 'dan Najeriya daga jihar Enugu ta bayyana bidiyon kanta da irin rayuwar da take yi a Najeriya
  • Kyakyawar matar ta nuna kanta tana ayyukan gida kamar wanki da shara kuma tace tana jin dadin zaman ta a kasar nan
  • Ta kara da bayyana irin farin cikin da take yi da mijinta yayin da ta sanar da cewa burinta ya cika tunda ta auri 'dan Najeriya

Wata baturiya wacce ta auri dan Najeriya ta bayyana yadda take jin dadin zama da mijin ta dan Najeriya. Ta wallafa bidiyon kanta tana ayyukan gida a Najeriya tare da wasu matan kauye.

Yayin wallafa bidiyon, tace gaskiya akwai sauki sabo da rayuwar Najeriya saboda tun farko ta saba yin ayyukan gida.

Baturiya a Kauye
Bidiyo: Baturiya da ta aura 'dan Najeriya tace tana jin dadi, ta shiga cikin matan kauye tana shara da wanki. Hoto daga @realhousewifeofnigeria
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Idan da mai bukata, a neme ni: Bidiyon dirarriyar BaAmurkiya da tace 'dan Najeriya take son aure

Kamar yadda kyakyawar matar wacce aka yi wa lakabi da sunan mace ta gari, tace tana jin dadin zaman ta a kasar nan.

Ta kara da bayyana cewa mijin ta dan asalin jihar Enugu ne kuma ya kasance miji nagari tun bayan da suka yi aure.

Ta wallafa bidiyon ne ta TikTok a shafi mai suna @realhousewifeofnigeria.

Jama'a sun yi martani

@jbforever48 yace: "Ba wai kokarin zolaya ba, meye amfanin share dattin? Na dade ina son sanin haka."
@gloryjimmy0 tace: "Allah yayi miki albarka matar mu ta Najeriya, ina alfahari dake mace tagari."
@iammrspacillalove tace: "Ina addu'a Ubangiji ya sanyawa auren ki albarka, nima na janyo mijina zuwa Amurka shekaru 9 da suka gabata kuma muna zaman lafiya. Shekarunmu goma da aure."
@skayonyon ya tambaya: "Daga wacce kasa kike? Kai tsaye zan tafi kasar ku, wannan babbar albarka ce."
@musbau55 yace: "Wannan abun birgewa ne ka ga mace haka. Wacce ke zama a Amurka tana irin wannan. Ina yi muku addu'a, Allah yasa muku albarka a auren ku."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matar aure ta bai wa mai kayan miya kyautar N1m, ta bayyana alherin da yayi mata a baya

Hotuna: Bayan wata 5 da aure, fitacciyar 'yar siyasa ta haifawa mijinta santalelen 'da namiji

A wani labari na daban, Kyawawan hotunan fitacciyar 'yar siyasa kuma tsohuiwar 'yar takarar gwamnan jihar Kogi, Natasha Akpoti, yayin da ta haifa yaro namiji sun bayyana.

Kamar yadda aka gano, matashiyar 'yar siyasan ta haifa 'danta na farko ne a ranar 12 ga watan Yulin 2022 a wani asibiti dake Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng