Idan da mai bukata, a neme ni: Bidiyon dirarriyar BaAmurkiya da tace 'dan Najeriya take son aure
- Wata zukekiyar budurwa 'yar kasar Amurka ta janyo cece-kuce bayan ta tallata kanta ga mazan Najeriya kai tsaye
- A bidiyon da ke ta yawo a shafukan sada zumunta, dirarriyar budurwar tace bata da miji kuma tana neman 'dan Najeriya da zasu yi aure
- Ta kara da cewa, tana da aikin ta mai kyau, gidan kanta kuma tana son namiji da zai koma Amurka don ta inganta rayuwarsa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Wata budurwa 'yar kasar Amurka ta bayyana bukatarta fili ta son aure namiji 'dan Najeriya. Budurwar da ke bukatar mijin, an ganta a wani bidiyo da ma'abocin amfani da Facebook, Bala Baba Dihis ya wallafa tare da yin tsokaci da:
"Mazan Najeriya... Tace tana da mazaunai fa... Ku hanzarta..."
Kamar yadda tsokacinsa ya bayyana, budurwar ta bayyana mazaunanta a karshen bidiyon domin jan hankalin mazan.
Da murmushi a fuskarta, budurwar tace tana neman namiji 'dan Najeriya da ke son komawa Amurka kuma su karashe rayuwarsu tare.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Budurwar ta kara da cewa, tana da aiki mai kyau kuma tana tabbatar wa da duk namijin da ya aureta rayuwa mai inganci. Tayi kira ga maza masu bukata da su tuntubeta kai tsaye.
Abinda take cewa: "Mazan Najeriya, ina neman miji wanda yake son dawowa wurina a Amurka kuma ya kare rayuwarsa da ni.
"Ina da gidana na kaina, ina da aiki mai kyau kuma ina son ka dawo nan domin samun ingantacciyar rayuwa. Idan akwai mai bukata, ya neme ni. Kuma, ina da mazaunai."
Latsa nan don ganin bidiyon.
Jama'a sun yi martani
John David yace: "Mata marasa tunani ne ke cewa garabasa ta samu ga mazan Najeriya, kowa ya san mu da son mazaunai. a tunaninku mazan Najeriya zasu bi wannan matar ne saboda mazaunanta?"
Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, Jarumar fim mai shekaru 52
Allison Charles Ajuluchukwu yace: "Ina kwatanta yadda za a dinga tuntubarta. Tabdijan, ta yuwu shafinta ya rushe ma. Da yawa daga cikin masu bukatar zasu kasance mazan aure."
Godslove Peter yace: "Toh fah, idan da ace kina da wannan kimar, mazan Amurka ne zasu yi rububi. Ba zaki dinga neman damar auren miji n kasa dake ba daga kasar nan. Dauka shafaffen cikin ki da 'ya'ya shida ki cigaba da sabgarki."
Asali: Legit.ng