Safarar Sassan Jikin Mutum: Za A Iya Yi Wa Ekweremadu Da Matarsa Daurin Rai Da Rai A Birtaniya

Safarar Sassan Jikin Mutum: Za A Iya Yi Wa Ekweremadu Da Matarsa Daurin Rai Da Rai A Birtaniya

  • Ta yi wu a yanke wa Sanata Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice hukuncin daurin rai da rai idan aka same da laifin safarar sassan jikin dan adam
  • Dokar Birtaniya ta Modern Slavery Act, 2015 (MSA 2015) ta tanadi laifi mai tsauri da ya kama daga daurin watanni 12 a gidan gyaran hali har zuwa daurin rai da rai a gidan gyaran hali
  • An gurfanar da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawar na Najeriya da matarsa a kotu a ranar Alhamisa a Birtaniya kuma ba a belinsu ba bayan kotun ta fara sauraron karar

Ana iya yi wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice daurin rai da rai idan aka same su da laifi kuma aka yanke musu hukunci mafi tsauri a dokar Birtaniya ta Modern Slavery Act, 2015 (MSA 2015).

Kara karanta wannan

Har yanzu ban samu wata sanarwa a hukumance daga ubangidana ba - Hadimin Ekweremadu

An kama mata da mijin ne aka kuma gurfanar da su a kotun Birtaniya kan zargin hannu cikin cire sassan dan adam a kotun Majistare da ke Uxbridge a ranar Alhamis.

Ekweremadu da matarsa Beatrice.
Safarar Sassan Jikin Bil Adama: Za A Iya Yi Wa Ekweremadu Da Matarsa Daurin Rai Da Rai A Birtaniya. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Yan sandan Landan sun ce sun fara bincike kan mutanen biyu ne bayan jami'an tsaro sun ankarar da su kan laifukan karkashin dokar bautarwa na zamani a Mayun 2022.;

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta rahoto cewa MSA 2015 ta yi hani da cire sassan dan adam, kuma ana hukunci har na daurin rai da rai idan an samu mutum da laifin.

Wani sashi na dokar ta ce:

"Karkashin s 2, mutum ya aikata laifi idan ya shirya ko ya taimaka wa wani ya yi tafiya da nufin a cire masa sassa. Ba banbanci ko mutumin ya amince ya yi tafiyar, ko yaro ne ko babba.

Kara karanta wannan

Layukan Wayan Ekweremadu Da Na Kakakinsa A Kashe, Yayin Da Aka Kama Shi Da Matarsa A Landan

"Karkashin s 3 na MSA 2015, cin zali ya kunshi: bautarwa, da tilasta wani yin aiki, cin zarafi (wanda ya kunshi aikata laifi karkashin s 1(1)(a) na dokar kare yara ta 1978. (hotuna rashin ɗa'a na yara), ko Pt 1 na SOA 2003 (misali cin zarafi ko cin zali); cire sassan jiki inda aka tsamani, bukata ko neman ya yi wani abu da ke matsayin laifi a karkashin sa 32 ko 33 na kundin dokar Hana Safarar Sassan Dan Adam ta 2004 (hana cinikayyar sassan jikin dan adam da hana amfani da masu bada sassa da ransu); neman sassan ta hanyar tilas, yaudara; neman sassa daga yara da mutane masu rauni (misali masu matsalar ƙwaƙwalwa, bukata na musamman)."
Ta kara da cewa duk wanda aka samu da laifin "safarar sassan dan adam za a iya yanke masa hukuncin daurin watanni 12' a gidan yari da/ko tara wanda ba a kayyade ba," ta kara da cewa "idan an tabbatar da laifi, ana iya yanke hukunci mafi girma na daurin rai da rai."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164