'Ta ya 'yan mata ke samun masoya?' Wata zankadediyar yan Najeriya ta koka kan rashin saurayi
- Wata budurwa yar Najeriya ta koma zama a Burtaniya shekara Bakwai da suka shuɗe amma har yau babu wanda ya nemi su fita
- Lamarin ya dame ta har ta kai ga ta ta nemi abokanan aikinta ta tambaye su ko akwai wani abu da ba dai-dai ba a tattare da ita
- Budurwar da zuciyarta ta karaya ta bayyana damuwar da take ciki a kafar sada zumunta tare da neman mutane su bata shawara yadda zata samu masoyi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya cikin damuwa ta yi ƙorafi game da zama ita kaɗai da rashin samun masoyi bayan shafe shekaru a Burtaniya.
A cewarta, ta kwashe shekara 7 a UK kuma duk tsayin lokacin nan tana rayuwa a can ba bu wanda ya taba fuskantarta don su ƙulla alaƙar soyayya.
Da take ba da labarinta a kafar sada zumunta, zankaɗeɗiyar budurwar ta bayyana yadda yanayin ya dameta a zuciya har ta gaza ɓoye wa, ta nemi abokanan aikinta su bata shawara.
Budurwan ta tambaye su ko tana da wata matsala ne, amma suka ce mata ba haka bane kuma suka sanar da ita cewa suma a halin da suka tsinci kansu kenan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Samun masoyi a kasar waje abu ne mai matuƙar wahala
Ƙawayen wurin aikin sun kyalkyala mata dariya yayin da suke gaya mata samun masoyi a ƙasar waje ba abu ne mai sauki ba musamman ma a Burtaniya.
A wani bidiyo da shafin @Instablog ya wallafa, matashiyar budurwan ta bukaci mutane su koya mata yadda zata samu saurayi.
A kalamanta ta ce:
"Abokai shekarata 7 kenan a UK ba'a taba samun wata rana ɗaya da wani ya tsayar da ni a hanya ba don ya gabatar da soyayyarsa gare ni. Saboda haka na tambayi ƙawayena a wurin aiki me yuwuwa ina da wata matsala."
"Amma suka mun dariya sannan suka ce mun haka ke faruwa a ko ina. Ina son na sani, wai mutanen da ke UK ya kuke haɗuwa da masoya? Muna son sani, mun gaji da zaman kaɗaici."
Mutane sun maida martani
Kamara Jake tace:
"Nima ina bukatar wani ya zo ya fitar dani daga kaɗaicin nan dan Allah."
Jittymars ya ce:
"Haba dan Allah ki dawo gida da yuwuwar wani ya zo yana neman ki."
Daringo Abel ta rubuta cewa:
"Wannan gaskiya ne tana faruwa, ina da ƙawaye a kasashen wajen da suka faɗa mun irin haka ke faruwa da su."
Chiomzy Okafir ya kara da cewa:
"Ki kokarin gyara gashin kan ki sannan ki dawo mu baki shawarin yadda zaki yi."
A wani labarin kuma Yan Najeriya sun yi ca kan wani lauya da ya ce mai gidan haya ba zai ƙara kuɗi ba da sai izinin 'yan haya
Tsautsayi: Kotu ta ci tarar wani matashi ta ɗaure shi a gidan Yari saboda rubutu kan korona a Facebook
Wani lauya a Najeriya ya haddasa cece-kuce yayin da ya yi ikirarin cewa masu gidajen haya ba su da ikon ƙara kudi sai yan haya sun amince.
Lauyan mai suna @Egi_nupe_ ya ce idan mai gidan ya matsa sai ya ƙara kuɗin ba tare da yarjejeniya ba, masu haya su nemi gargaɗin tashi.
Asali: Legit.ng