Nisan kwana: Yadda fasinjan da bai iya tuki ba ya ceto jirgin da direbansa ya rikice a sama

Nisan kwana: Yadda fasinjan da bai iya tuki ba ya ceto jirgin da direbansa ya rikice a sama

  • Rahotannin da muke samu daga kasashen ketare, sun bayyana yadda wani lamari mai ban al'ajabi ya auku
  • Wani direban jirgin sama ya samu makuwa a sama, lamarin da ya kai ga fasinja ya taimaka masa wajen sauko da jirgin
  • Rahoton da muka hada ya bayyana yadda lamarin ya faru da yadda fasinjan ya nemi taimakon cibiyar kula da jiragen sama

Florida, Amurka - Wani fasinjan da bai iya tukin jirgi ba ya sauko da jirgin da rikice a sama a yankin Florida bayan gazawar direba wajen shawo kan jirgin, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta tarayya na gudanar da bincike kan lamarin, wanda ya faru da yammacin ranar Talata. An yi imanin cewa mai yiwuwa matukin jirgin ya sami matsalar lafiya ne mai neman taimakon gaggawa.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Yadda aka ceto jirgi daga fadowa
Nisan kwana: Yadda fasinjan da bai iya tuki ba ya ceto jirgin da direbansa ya rikice a sama | Hoto: theguardian.com
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa da hukumar ta FAA ta fitar ta ce fasinjoji biyu na cikin jirgin mai lamba Cessna 208 lokacin da matukin jirgin ya samu "rashin lafiya".

Yadda lamarin ya faru

Fasinja daya daga ciki ne ya tuko jirgin mai zaman kansa cikin kwanciyar hankali zuwa filin jirgin saman Palm Beach.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sakon sauti na LiveATC.net, fasinjan ya gaya wa cibiyar kula da zirga-zirgar jiragen sama cewa:

"Ina cikin wani mummunan yanayi a nan. Matukin jirgi na ya shiga wani yanayi ba daidai ba kuma ba ni da masaniyar kan yadda zan tuka jirgin."

Da aka tambaye shi kan halin matukin jirgin ke ciki, fasinjan ya ce:

“Bai san inda yake ba. Ya fita daga hayyacinsa."

Daga nan cibiyar ta tattauna dashi tare da ba shi kwatancen yadda zai tuko jirgin tare da sauka cikin kwanciyar hankali, kamar yadda CNN ta naqalto yadda tattaunawar ta kasance.

Kara karanta wannan

Mafi girman laifi ta yi: Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi

‘Yan bindiga sun tsare mai tsohon ciki, ta na kokarin nakuda, su na neman kudin fansa

A wani labarin, a garin Jalingo da ke jihar Taraba, masu garkuwa da mutane sun rike wata Baiwar Allah duk da ganin irin mawuyacin halin da ta samu kan ta.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa wannan mata mai dauke da juna biyu ta shiga nakuda, amma ‘yan bindigan da suka kama ta sun ki fito da ita.

Asali ma sai aka ji labarin cewa su na neman a aiko masu kudin fansa idan ana so ta samu ‘yanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.