Hukumomin Saudiyya sun haramta wa mazan kasar auren matan Pakistan

Hukumomin Saudiyya sun haramta wa mazan kasar auren matan Pakistan

  • Hukumomin Saudi sun haramta wa mazan kasar auren mata daga Pakistan, Bangladesh, Chadi da Burma, anyi hakan ne don rashin ba wa mazan Saudi damar auren mata daga kasashen ketare
  • Wajibi ne mazan Saudi dake son auren mata daga kasashen ketare su samu shaidar amincewa daga sananniyar hukumomin gwamnati, tare da shigar da bukatar auren a kafar da ta dace
  • Daraktan 'yan sanda Makkah ya ce duk wani neman auren da ba a masarautar ba zai dau tsawon lokaci tare da tsananta lura da bin matakai daban-daban kafin a amince ko a yi watsi da batun

Saudi Arabia - An haramta wa mazan Saudi auren daga auren matan Pakistan, Bangladesh, Chadi da Burma.

Life in Saudi ta ruwaito cewa, an sanar da hakan ne don hana mazan Saudi karfin guiwar auren mata daga kasashen ketare.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Hukumomin Saudiyya sun haramta wa mazan kasar auren matan Pakistan
Hukumomin Saudiyya sun haramta wa mazan kasar auren matan Pakistan. Hoto daga lifeinsaudiarabia.net
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan kasar Saudi dake son auren matan kasashen ketare, da farko dai za su nemi takardar shaidar amincewa daga sananniyar hukumomin gwamna, tare da shigar da bukatar auren a inda ya dace.

Manjo janar Assaf Qureshi, wanda shi ne daraktan 'yan sandan Makkah ya ce, duk wani shigar da bukatar aure daga wajen masarautar zai bi ta hanyoyin lura da tsanani kafin a amince ko a ki amincewa da shi.

Daga nan ne kwamitin za ta yanke shawarar amincewa ko rashin amincewa da hakan.

Haka zalika, dole ne lamarin wajen ganin an yanke hukunci mai kyau, kwamitin na bukatar dogon nazari a kan shigar da bukatar da aka yi.

Ana dab da Iftar, magidanci a Saudiyya ya kone iyayensa, iyalinsa da gidansa kurmus

A wani labari na daban, ana dab da buda baki, wani mutumi ya garkame mahaifinsa, mahaifiyarsa, 'dansa da 'diyarsa, wadanda ke azumi a gidan a Saudiyya gami da banka wa gidan wuta.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Wutar ta fara ci ne sanadiyyar man fetur da aka antaya wa gidan, gami da banka wa gidan wuta, wanda ya lashe rayukan mutane hudu: mahaifinsa, mahaifiyarsa, karamin yaronsa da 'diyarsa.

Mummunan lamarin ya auku ne a Safwa, kusa da Qatif, inda gobarar ta balle ana dab da buda baki. Iyalin basu tsira daga kunar wutar ba, inda ya rufesu da gan-gan a wani daki don hana su guduwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng