Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya biya N16m, ya ceto Bayin Allah daga kurkuku a Ramadan

Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya biya N16m, ya ceto Bayin Allah daga kurkuku a Ramadan

  • Gidauniyar Muhammadu Sanusi II Foundation ta yi sanadiyyar da aka saki wasu fursunoni a Kano
  • Mutane 59 za su yi bikin idi a gaban ‘yanuwansu bayan an biya bashin kudin da ya sa aka daure su
  • Wannan gidauniya ta saba ‘yanta masu zaman kason da suka yi kananan laifin da bai kai, ya kawo ba

Kano - Muhammadu Sanusi II Foundation, wata gidauniya da tsohon Sarkin Kano ya kafa, ta ceto wasu mutane da-dama da su ke gidajen gyaran hali.

Jaridar Daily Nigerian ta fitar da rahoto da ya nuna cewa gidauniyar tsohon sarki Muhammadu Sanusi II ta kubutar da wasu mutum 59 da ke daure.

Gidauniyar Khalifa ta biya tsabar kudi har N16,820,370 domin warware bashi da tarar da ke kan wadanda su ke zaman kason da nufin sus amu ‘yanci.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC a yankin Kaduna

Rahoton ya ce wadannan mutane da suka aikata kananan laifuffuka su na tsare ne a gidajen gyaran hali na Kurmawa da Goron Dutse a jihar Kano.

Babban mai kula da gidauniyar, Mujitaba Abba ya shaidawa manema labarai a garin Kano cewa Muhammadu Sanusi ll ya bada umarnin ceto fursunonin.

An fito da mutum kusan 60

Abba ya ce a gidan yari na Kurmawa, Mai martaba Muhammadu Sanusi ll ya yi dalilin fitowar mutane 26 bayan ya biya N4,466,500 da ke kan wuyansu.

Tsohon Sarkin Kano
Mai Martaba Muhammadu Sanusi II Hoto: Majeeda Studio
Asali: Instagram

Haka zalika Khalifan na darikar Tijjaniyya a Najeriya ya biya N11,380,770 domin a sallami mutane 33 da ke tsare a gidan gyara hali na unguwar Gorondutse.

“Mun fahimci cewa akwai fursunoni da-dama da ke tsare a dalilin bashi da wasu kananan laifuffuka na sabani na tsakanin mutum da mutum.”

Kara karanta wannan

ICPC ta fallasa dabarar da ‘Yan Majalisa su ke yi, su na yin awon gaba da dukiyar talakawa

“Saboda haka, Mai martaba (Sanusi II) ya sauke nauyin bashi, tara da kudin da yake kan su, kudin ya kai N16,820, 370.” - Malam Mujitaba Abba.

Sai a kiyaye gaba kuma

A cewar Abba, tsautsayi ya jefa wasu daga cikinsu gidajen gyaran halin. Wasu kuma sun aikata laifuffukan, amma an ja kunnensu a kan fadawa gidan jiya.

Shugaban gidauniyar ya yi kira ga wadanda aka ceto su guji aikata abin da zai sake jawo masu dauri. Ba wannan ne karon farko da gidauniyar tayi haka ba.

Abin da ya jawo aka tsige ni - Sanusi

Kwanaki aka samu rahoto Malam Muhammadu Sanusi II ya yi bayanin abin da ya kai shi ga rasa kujerar gwamnan babban bankin CBN da sarautar gidan dabo.

Khalifa ya ce fadawa masu mulki gaskiya ne dalilin da ya sa aka sauke shi daga matsayinsa. Sanusi II ya ce ya yi gadon tsayawa kan gaskiya daga kakansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel