Dole kasashen Afrika su shiryawa muguwar yunwar da za a fuskanta - Shugaban bankin AfDB

Dole kasashen Afrika su shiryawa muguwar yunwar da za a fuskanta - Shugaban bankin AfDB

  • Shugaban babban bankin cigaban Afrika ya yi hasashen za ayi muguwar yunwa da tsadar abinci
  • Dr. Akinwumi Adesina ya ce yakin Rasha da Ukraine ya jawo kayan abinci sun tashi a duk Duniya
  • Tsohon Ministan gonan Najeriya ya yi kira ga kasashen Afrika su tashi tsaye, su shiryawa annobar

Shugaban babban bankin cigaban Afrika, Akinwumi Adesina ya fitar da jawabi yana cewa dole Afrika ta shiryawa matsalar kayan abinci da za a fuskanta.

Dr. Akinwumi Adesina ya ce yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine zai jawo yunwa a Duniya. Jaridar The Cable ta fitar da wannan rahoto a ranar Litinin.

A wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi, 24 ga watan Afrilu 2022, an ji cewa Dr. Adesina ya yi magana a game da Afrika a wajen wani taro da aka shirya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Graham Douglas, ya mutu

Shugaban bankin da aka kafa domin cigaban nahiyar ya bukaci a maida hankali a kan wannan annobar da sau daya rak ake ganin irinta a cikin shekaru 100.

A cewarsa, wasu kasashen Afrika sun gamu da annobar COVID-19, matsalar sauyin yanayi da sauran musiba wanda suka tabarbarar da tattalin arzikinsu.

Adesina ya ce Afrika mai karancin GDP a duk Duniya ta yi asarar ayyuka miliyan 30 saboda annobar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban bankin AfDB
Dr. Akinwumi Adesina Hoto: @akin_adesina
Asali: Twitter

Yakin Rasha v Ukraine

Da yake bayani a game da tasirin yakin Rasha-Ukraine, Adesina ya nuna tausayinsa ga mutanen Ukraine, ya ce ba za a iya tunanin wahalar da suke ciki ba.

Tasirin wannan yaki zai shafi sauran kasashen Duniya, har da nahiyar Afrika. Masanin tattalin ya ce daga yankin ne ake samun 30% na alkaman da ake ci.

A halin yanzu farashin alkalama ya tashi da sama da 50%, har abin ya kai kamar yadda kasashe suka sha wahala a lokacin da aka yi wahalar abinci a 2008.

Kara karanta wannan

Namijin duniya: Mutumin da ya hau babur daga Landan zuwa Legas ya shigo Afrika a rana ta 6 a tafiyarsa

Tun da takin zamani ya tashi...

Rahoton da jaridar ta fitar ya nuna cewa baya ga tsadar kayan abinci, farashin takin zamani ya yi sama, sannan kudin fetur da man dizil sun yi tsada a ko ina.

Tun da taki ya kara kudi, tsohon Ministan na Najeriya ya ce a saurari tsadar kayan abinci a kasashen Afrika. Nan da ‘yan watanni abinci za su kara tsada.

Kafin a shawo kan lamarin, dole sai mutanen Afrika sun dage wajen noma abin da za su ci. Adesina ya ce bai dace a rika roko ba, dole a nemo mafita a gida.

Volodymyr Zelensky da Putin

A kwanakin baya aka ji yadda shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya sa hannu, ya na rokon a sa kasar Ukraine a cikin ‘yan kungiyar EU ta tarayyar Turai.

Hadimin shugaban kasar, Sergii Nykyforov ya bada wannan sanarwa a shafinsa na Facebook. Irin haka ne zai sake kawo matsala tsakanin Zelensky da Rasha.

Kara karanta wannan

Daga Fara Magana a Facebook: Baturiya Ta Baro Amurka Ta Yi Wuff Da Wani Matashi a Najeriya, Hotunansu Ya Ɗauki Hankula

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng