Zanga-Zanga Ta Ɓarke Bayan Wani Ɗan Siyasa Mai Ƙyamar Musulunci Ya Ƙona Al-Ƙur'ani Mai Tsarki

Zanga-Zanga Ta Ɓarke Bayan Wani Ɗan Siyasa Mai Ƙyamar Musulunci Ya Ƙona Al-Ƙur'ani Mai Tsarki

  • Rikici ya barke a birnin Linköping da ke kasar Sweden yayin da fusattun musulmai suka fito suka nuna rashin jin dadinsu akan kone Al-Qur’ani mai tsarki da wani dan siyasa ya yi
  • Yayin rikicin, ‘yan sandan kasar sun yi yunkurin dakatar da jama’a daga yin zanga-zangar wanda sanadiyyar haka mutane uku suka jigata
  • Dan siyasar mai tattsauran ra’ayi da nuna tsana ga addinin musulunci da bakaken fata, Rasmus Paludan ne ya shirya gangamin da ya haddasa rigimar tun farko

Sweden - Birnin Linköping da ke gabar tekun gabashin Sweden ya rikice sakamakon wata hayaniya da ta hautsine tsakanin masu zanga-zanga don nuna fushinsu akan kona Al-Kur’ani mai girma da wani dan siyasa mai nuna tsana ga addinin musulunci ya yi da kuma ‘yan sandan kasar.

Kamar yadda BBC ta nuna, ‘yan sanda uku sun jigata sakamakon rikicin.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Gidan Ɗan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar APC Kwana 4 Bayan Sanar Da Takararsa

Zanga-Zanga Ta Ɓarke Bayan Wani Ɗan Siyasa Mai Ƙyamar Musulunci Ya Ƙona Al-Ƙur'ani Mai Tsarki
Sweden: Zanga-Zanga Ta Ɓarke Bayan Wani Ɗan Siyasa Mai Ƙyamar Musulunci Ya Ƙona Al-Ƙur'ani Mai Tsarki. Hoto: BBC Hausa.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumomin birnin Orebro da ke tsakiyar kasar sun nuna yadda mutane suka sake fita zanga-zangar bayan wani dan siyasa, Rasmus Paludan ya shirya gangamin nuna tsana da kyama ga bakaken fata da addinin musulunci.

Paludan dai dan siyasa ne mai asali biyu, da Sweden da kuma Denmark.

Ba wannan bane karon farko da Paludan ya fara haddasa rikici ba

Yayin gangamin farko, ‘yan sanda tara sun jigata. Sai dai an kama mutane biyu.

Kamar yadda BBC Hausa ta bayyana, ‘yan sandan sun yi yunkurin nuna aikinsu na bai wa mutane damar bayyana ra’ayinsu, ba tare da yin alkalanci wurin zaben wanda ke da gaskiya ko kuma akasinta ba.

Ba wannan bane karo na farko da Paludan ya haddasa rikici ba, a watan Nuwamban shekarar 2020, sai da hukumomin kasar Faransa suka fatattake shi daga kasar.

Kara karanta wannan

Harin 'yan bindiga a Plateau: Ya zuwa yanzu mun binne mutane 106, inji shugaban karamar hukuma

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164