Wasu barayi sun sace gadar karfe mai tsayin kimanin mita 20 a kasar Indiya

Wasu barayi sun sace gadar karfe mai tsayin kimanin mita 20 a kasar Indiya

  • Wasu barayi sun wani sata mai ban mamaki a kasar Indiya inda suka yi awon gaba da gadar karfe
  • Hukumomi sun bayyana cewa gadar mai dimbin tarihi na da nauyin ton dari biyar
  • Mai magana da yawun yan sanda yace an kadamar da bincike kan wannan gagarumar sata

Wasu gungun barayi sun tafka sata da tsakar rana inda suka yi awon gaba da gadar karfe mai tsayin mita 18.3 kan rafin Ara-Sone, garin Rohtas a gabashin kasar Indiya.

Kaakin Hafsan yan sanda, Subhash Kumar, wanda ya tabbatar da hakan ga AFP ya bayyana cewa barajin sun yi basaja ne da kayan ma'aikatan gwamnati.

Yace:

"Sun dauke gadar cikin wata babbar mota."

Kasar Indiya
Wasu barayi sun sace gadar karfe mai tsayin kimanin mita 20 a kasar Indiya Hoto: Wannan ba hoton gadar bane

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Mutane zasu fara cin ciyawa a Arewa saboda tsananin yunwa, Majalisar dinkin duniya

A cewar yan garin Rohtas, barayin sun kwashe kwanaki uku suna kokarin sace gadar.

Mazauna garin sunce sun yi mamakin yadda gadar tayi batar dabo duk da nauyinta ton 500.

An gina gadar ne a shekarar 1972 a garin Amiyawar.

Bincike ya nuna cewa barayi sun dade suna kokarin sace gadar tun lokacin da aka gina wata sabuwa na siminta kusa da ita.

Kakakin yan sandan, Kumar, ya ce tuni an sanar da masu siyan kayan karafuna su garzaya wajen hukuma idan suka ga wani da gadar.

Indiya ta maye gurbin Najeriya matsayin hedkwatar talauci na duniya

Kasar Indiya ta zarcewa Najeriya a matsayin kasar da tafi adadin mutane masu fama da talauci a fadin duniya.

Wannan ya bayyana bisa rahoton da World Poverty Clock (WPC) ta saki na shekarar 2022.

World Poverty Clock (WPC) wani shafin yanar gizo ne dake bibiyan adadin mutanen da suke fadawa talauci kulli yaumin a kasashen duniya.

Kara karanta wannan

Hotunan Kafin Aure Na Wata Zankadediyar Budurwa da Angonta Karami Ya Ja Hankali

Majalisar dinkin duniya ta yi ta'rifin talauci a matsayin gazawar mutum ya samu $1.90 (N800) a rana.

Bisa sabon rahoton WPC, yan kasar Indiya milyan 83 ne suka fada talauci a 2022, sabanin milyan 73 a shekarar 2018.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: