Dan Najeriya ya bude wurin abincin gargajiya a London, Turawa da bakar fata ke layin siya

Dan Najeriya ya bude wurin abincin gargajiya a London, Turawa da bakar fata ke layin siya

  • A halin yanzu wani mutumi dan Najeriya na cigaba da gudanar da fitattcen gidan saida abinci na gargajiya a wata anguwa a Landan wacce ake kira da Spitalfields
  • Mutumin mai suna Azeez ya ce ya bude gidan sai da abinci da suna 'yaran Najeriya guda 2,' tare da wani abokinsa, amma yanzu yana gudanar dashi shi kadai
  • A wani hoto da @lamOlajideAwe ya wallafa a Twitter, an ga wasu turawa na layin siyan dafa-dukan shinkafar Najeriya

Wani dan Najeriya mai suna Azeez ya fara aikin dafa shinkafar dafa-duka irin ta Najeriya a titin Landan, wanda yasa Turawa da dama suka yaba da irin dadin abincin.

A hoton da @IamOlajideAwe ya wallafa, anga wasu turawa na layin siyan abincin a gidan saida abinci.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Bidiyon busasshen tsohon da mutuwa ta mance dashi ya girgiza intanet

Dan Najeriya ya bude wurin abincin gargajiya a London, Turawa da bakar fata ke layin siya
Dan Najeriya ya bude wurin abincin gargajiya a London, Turawa da bakar fata ke layin siya. Hoto daga @IamOlajideAwe da 2 nigerian boys
Asali: UGC

Turawa na kaunar shinkafa, shiyasa su tururuwar zuwa siya.

Yayin hira a kafar sada zumunta da wakilin Legit.ng, Azeez ya bayyana yadda ya fara gudanar da siyar da abincin tare da wani, amma yanzu shi kadai ke gudanarwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Azeez ya ce: "Ni dan Legas ne daga Surulere. Muna zama ne a Landan, saboda haka muka yanke shawarar kawo abincin cikin birnin. Mu biyu muka fara, amma yanzu da kaina nake yi."

Yayin da @lamOlajide ya wallafa labarin, ya janyo masa jinjina daga 'yan Najeriya da dama, inda suka yi ta yabawa da irin fatutukarsa.

Hakan yasa 'yan Najeriya hanzarin yin tsokaci don tofa nasu albarkacin. Ga wasu daga cikin tsokacin da suke fadi:

@iam_FPresident ya ce: "Wannan abu yayi kyau. Ina fatan zamu samu karfin guiwar saida abinci a Najeriya a matsayinmu na matasa. Ameen."

Kara karanta wannan

Korarren Liman Nuru Khalid: A da mimbarin masallacin Apo ne cibiyar kamfen din Buhari

@Nedujizzy1 yayi martani: "Ya kamata in bi ka in gani. Mutanen da kema wasu addua don su rayu da gaske, wannan abun ko da basa son shi ku sake wallafa shi, muna ganinku."
@Temitope_AA ta ce: "Turawan ne ke layin siyan shinkafa dafa-duka?"
@MaziAkuche ya ce: "Hakan yayi daidai. Wannan neman na kai ne. Ku cigaba gayu. Wasu hanyoyin zasu bude don bunkasa."

Gwarzon namiji: Matashin da yayi wuff da mata 9 a rana 1 yace yana son karin wasu 2

A wani labari na daban, wani matashi mai suna Arthur O Urso, wanda ya auri mata 9, ya bayyana cewa yana son ya auri wasu mata biyu don kai adadin matansa zuwa 10 tunda daya na son fita.

Mirror.co.uk ta ruwaito cewa, dan asalin kasar Brazil din ya zama abin burgewa a intanet a shekarar 2021 bayan ya bi kanun labarai bayan ya tare da mata 9 a lokaci daya a wani karamin biki da ya gudana a birnin São Paulo na kasar Brazil.

Kara karanta wannan

Sun Gane Shayi Ruwa Ne: 'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

Mahaifin yaro dayan da farko yana tare da matarsa ta farko mai suna Luana Kazaki amma daga bisani suka kulla aure da ita yayin da ya auri sauran 8 a lokaci daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng