Gwamnatin Malaysia za ta daure ko cin tarar 'yan kasa da ke cin abinci da rana a Ramadan
- Gwamatin Malaysia ta sanar wa Musulman da keda lafiya amma suke cin abinci da rana cikin watan Ramadana cewa za a fara cin su tara ko jefasu gidan yari ko duka biyun
- Ahmad Zakiyuddin ya bayyana yadda kungiyar musuluncin zata fara cin mutane tara ko gidan yari a karo na farko, sannan za ta ninka hukunci idan aka sake maimaitawa
- A cewar mataimakin ministan, dokar ta haɗa da masu siyar wa da gyandaye abinci a bainar jama’a a cikin watan Ramadana mai alfarma
Gwanatin ƙasar Malaysia ta bada sanarwan cewa za a kama Musulman da ke da isashshen lafiya amma suke ci da sha a bainar jama'a lokacin azumin watan Ramadana, gami da cinsu tara ko kai su gidan yari ko kuma duka biyun.
Penang, babban mataimakin minista, I Datuk Ahmad Zakiyuddin ya bayyana yadda za a gurfanar da masu karya doka karkashin sashi na 15 na kundin shari’ar Penang na shekarar 1996, The Islamic Information ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa lokacin Ramadana, wata jiha a Malaysia za ta aiwatar da aikin, wanda shine ɗaya daga cikin kokarin mulkin Musulunci don faɗakar da Musulmai da kuma gayyatarsu don yin bauta a watan mai albarka tare.
Ana sa ran wannan aikin za a aiwatar ya kawo karshen halayen da basa girmama watan Ramadana, irin su gangancin ci da sha a bainar jama’a ba tare da ciwo ba.
Ya kamata a san cewa, idan aka aikata laifin a karo na farko, za a ci mutum tarar da ba za ta wuce RM1,000 ko zaman gidan gyaran hali na tsawon watanni shida ko kuma duka biyun.
Amma, idan mutum ya sake karya dokar za a ci shi tarar RM2,000 ko shekara daya a gidan gyaran hali ko kuma duka biyun, The Islamic information ta ruwaito.
A cewar Ahmad Zakiyuddin, wanda shi ne shugaban kungiyar musulunci ta Penang (MAINPP), doka ta 15 ba tana aiki kawai a kan masu karya doka, wadanda ke ci da sha a bainar jama’a a Ramadana ba, harda waɗanda ke saida abinci, abin sha, sigari, da sauran abubuwan da suka yi kama da haka ga Musulmai a bayyanannun wurare cikin watan Ramadana.
Ya ce sashin lamurran da suka shafi musulunci na Penang (JHEAIPP), Hukumar kula da birnin Penang (MBPP), Hukumar kula da birnin Seberang Perai (MBSP), da sashin kula da lafiya na Penang da marabar JHEAIPP Halal zasuyi aiki tare don ganin sun kawo karshen masu karya doka.
Ya kara da bayyana yadda a halin yanzu, JHEAIPP suka samu kusan na'urori 120 da zasu dinga sa ido. Bugu da ƙari, aikin zai maida hankali game da tsaftar wurare da yadda ake kula da abinci, tare da lasisin samar da abincin, da sauran mahimman abubuwan dake ƙarƙashin tsari da dokokin.
Ahmad Zakiyuddin ya rufe jawabinsa da sa ran masu aiwatar da aikin za su yi nasara wajen faɗakarwa Musulman Penang, yadda a Ramadan wannan shekarar zai zama Ramadanan da yafi sauran.
Asali: Legit.ng