Yakin Rasha: An kashe Sojin Ukraine 1300, Sojojin Rasha sun yi luguden bam a masallaci

Yakin Rasha: An kashe Sojin Ukraine 1300, Sojojin Rasha sun yi luguden bam a masallaci

  • Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce sun kashewa Rasha sojoji kusan 1300 zuwa yanzu
  • A cewar Mr. Volodymyr Zelensky kafin sojan Ukraine daya ya mutu, sai an kashewa Rasha sojojinta 10
  • Ana zargin Rashawa da hallaka masu fararen kaya sama da 1500 a cikin kwanaki biyu a garin Mariupol

Ukraine - Kimanin sojoji 1, 300 ne kasar Ukraine ta rasa tun daga lokacin da Rasha ta shigo mata da yaki zuwa yanzu. Volodymyr Zelensky ya bayyana wannan.

AP ta rahoto shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky a ranar Asabar yana cewa sun rasa dakaru 1, 300 a sanadiyyar yakin da ake gwabzawa.

Wannan ne karon farko da Volodymyr Zelensky ya fadawa Duniya adadin rashin da aka yi a yakin.

Kara karanta wannan

Obasanjo: Ban Nemi Mulki Ba, Mulki Ne Ta Riƙa Bi Na A Guje

Sojoji nawa Rasha ta rasa?

Kusan makonni biyu da suka wuce ne gwamnatin Rasha ta ce sojojinta kusan 500 sun hallaka. Channels TV ta ce har yanzu ba a kara jin labarin adadinsu ba.

Shi dai shugaban Ukraine, Zelensky yana ikirarin sun kashe sojojin Rasha kusan 12,000. Duk da haka, Zelensky yana ganin wadanda aka kashe sun yi kadan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sojojin Rasha fiye da 150, 000 suka shigo Ukraine bayan yaki ya barke tsakaninsu a farkon watan Maris. Tun daga lokacin kasar Ukraine ba ta sake zama lafiya ba.

Masallaci
Masallacin Sultan Suleiman the da Mai dakinsa Roxolana Hoto: @MFA_Ukraine
Asali: Twitter

Ana cigaba da kai hari a Ukraine

A ranar Asabar ne dai sojojin saman Rasha suka tarwatsa babban filin jirgin da ke Vasylkiv. Wannan gari ya na kusan kilomita 40 ne daga babban birnin Kiev.

Dama can dakarun Rasha sun yi luguden wuta a garuruwan Irpin da Bucha da ke yankin Arewa maso yammacin Ukraine, sun dumfari yankin Arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sojojin Rasha sun kashe wani fitaccen dan jaridar Amurka a Ukraine

Bam a Masallacin Sultan Suleiman

Wani rahoto da ya fito daga jaridar The Hill ya bayyana cewa rundunar Rasha sun tada bama-bamai a wani masallaci da ke yankin Mariupol, kasar Ukraine.

Kamar yadda gwamnatin Ukraine ta bada sanarwa a karshen makon jiya, wadanda aka rutsa a wannan harin sun hada da wasu Turkawa da ke samun mafaka.

Akwai kananan yara da mata sama da 80 a cikin Masallacin na Sultan Suleiman da matarsa Roxolana a lokacin da sojojin Rasha suka kai harin bama-baman.

Ba a iya tantance adadin wadanda suka mutu da wadanda suka jikatta a sakamakon harin ba. Dmytro Kuleba ya ce an kashe masu farar hula 1500 a Mariupol.

Tsadar abinci a Najeriya

An ji cewa manoma su na kokawa kan yadda buhun takin zamani ya yi matukar tsada a kasuwa. Idan har farashin taki bai yi kasa ba, kayan abinci za su kara tsada.

Kara karanta wannan

Sojojin Ukraine sun hallaka wani Hafsun Sojan da kasar Rasha ta ke ji da shi a filin yaki

Yakin Rasha v Ukraine yana cikin abubuwan da zai taimaka wajen kawo matsalar. Ukraine ta na noman abinci sosai, kuma ta na samar da sinadaran hada taki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng