Bayan shekaru 54, Bakano ya kafa tarihin zama Shugaban kungiyar Injiniyoyin Duniya
- A ranar Laraba Mustafa Balarabe Shehu ya zama sabon shugaban kungiyar nan WFEO ta Duniya
- Rahotanni daga kasashen waje sun tabbatar mana da cewa Shehu ne ya lashe zaben da aka shirya
- Injiniya Mustafa Shehu ya fito ne daga Kano, shi ne mutumin Sahara na farko da zai rike WFEO
Costa Rica - Kamar yadda WFEO ta bayyana a shafinta na Twitter, Mustafa Balarabe Shehu FNSE FAEng ya lashe zaben sabon WFEO da aka yi a makon nan.
Sanarwar da aka fitar a Twitter a ranar Alhamis, 10 ga watan Maris 2022 da kimanin karfe 1:00 na dare ya tabbatar da nasarar ‘Dan Najeriya a wannan zabe.
Kungiyar Injiniyoyi da masu zayyana na reshen kasar Kosta Rika su ka gudanar da wannan zabe.
"Muna taya Engr Mustafa B. Shehu daga Najeriya murna, wanda ya zama zababben shugaban kungiyar WFEO a taron da aka yi a San Jose, Costa Rica.
Kungiyar by CFIA - Colegio Federado de Ingenieros y de Arquitectos de Costa Rica ta shirya wannan zabe @ColegioFederado #SDGs #Agenda2030."
‘Dan Najeriya ya bar tarihi
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa WFEO ce babbar kungiya mai zaman kanta a Duniya ta Injinyoyi.
Wannan ne karon farko da aka samu wani mutumin Sahara daga nahiyar Afrika da ya dare kan wannan kujera. Shehu ya fito ne daga Kano a Arewacin Najeriya.
Kamar yadda wani tsohon hadimin gwamnan Kano ya bayyana a Twitter, idan Mustafa Balarabe Shehu ya yi nasarar karya wannan tarihi mai tsawon shekara 54.
Wanene Mustafa B. Shehu?
An haifi sabon shugaban na WFEO a shekarar 1963. Jaridar Abusites ta ce mahaifin Injiniyan watau Alhaji Shehu Salihu ya rasu ne a lokacin yana karamin yaro.
A haka ya samu damar yin karatu har ya zama injiniyan wuta a Jami’ar ABU Zaria a 1985. Shehu ya yi aiki da wurare da-dama kafin ya bude kamfani na kansa.
Injiniya Shehu ya shugabanci NSE a reshen Kano da mataki na kasa da kungiyar Injiniyoyin Afrika. Kafin yanzu ya rike kujerar mataimakin shugaban WFEO.
Da yake jawabi a shafinsa, babban Injiniyan ya mika godiya ta musamman ga ‘yanuwa da abokan arziki da suka taimaka masa da addu’o’i da goyon baya a zaben.
Zaman Shehu shugaba a WFEO
Ku na da labari cewa a Ranar Juma’a, 22 ga Watan Nuwamban 2019, Injiniya Mustafa Balarabe Shehu ya yi nasarar zama mataimakin shugaban kungiyar WFEO.
Shehu ya yi karatunsa a Kano, sannan ya tafi Makarantar gwamnati ta Kaduna domin sakandare. Daga nan kuma ya zarce zuwa fitacciyar jami’ar nan ta ABU Zariya.
Asali: Legit.ng