Injiniya Mustafa Balarabe Shehu shi ne sabon Mataimakin Shugaban WFEO

Injiniya Mustafa Balarabe Shehu shi ne sabon Mataimakin Shugaban WFEO

A Ranar Juma’a, 22 ga Watan Nuwamban 2019, Injiniya Mustafa Balarabe Shehu ya yi nasarar zama mataimakin shugaban kungiyar WFEO ta majalisar kwarrun Injiniyoyi ta Duniya.

Babbar kungiyar Duniyar ta zabi Mustafa Balarabe Shehu ne a wajen taron mako guda aka shirya a cikin Watan nan domin Injiniyoyin kasashe a Birnin Melbourne da ke kasar Australiya.

Abin ban sha’awar shi ne, Balarabe Shehu Mutumin Arewacin Najeriya ne wanda ya fito daga jihar Kano. Wannan fitaccen Injiniyan, kwararre ne wajen kai wutan lantarki cikin kauyuka.

Shehu ya yi karatunsa a Kano, sannan ya tafi Makarantar gwamnati ta Kaduna domin sakandare. Daga nan kuma ya zarce zuwa fitacciyar jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke Garin Zariya.

A shekarar 1985, Mustafa Shehu ya kammala Digiri a bangaren fasahar lantarki, sai ya zarce zuwa bautar kasa a ma’aikatar lantarki ta Enugu. A 1986 ya koma wani kamfanin wutan a Legas.

Bayan wannan kokari da Injiniya Mustafa Shehu ya yi ne aka bukaci ya dawo gida Kano domin ya yi aiki da kamfanin wutan lantarki na jihar, bayan wasu shekaru ya ajiye wannan aiki.

KU KARANTA: Dr. Abdullahi Balarabe Shehu ya samu lambar yabo daga sarauniyar Ingila

Daga ajiye aikin gwamnati, Mustafa Shehu, ya kafa kamfaninsa mai suna MBS Engineering LTD, wanda a baya aka sani da Amal Engineering. Yanzu haka shi ne shugaban wannan kamfanin.

Kamar yadda mu ka samu labari Injiniya Mustafa Balarabe Shehu ba bako bane a cikin tafiyar kungiyoyin Masana harkar fasaha domin ya rike mukamai iri-iri kafin samun wannan matsayi,

Shehu ya rike duka mukaman Mataimakin shugaba na kungiyar Injiniyoyi watau NSE na reshen Kano daga 2006 zuwa 2011. Daga baya ya kai ga zama shugaban kungiyar na reshen Kano.

A 2012 aka zabi wannan Bawan Allah a matsayin shugaban kungiyar NSE na Najeriya gaba daya. A 2016 ne Mustafa Shehu ya sauka daga kujerar shugaban kungiyar Injiniyoyin Nahiyar Afrika.

Yanzu wannan fitacce kuma kwararren Injiniya zai shiga cikin manyan shugabannin kungiyar Injiniyoyi na Duniya. WFEO ita ce Majalisar koli a sha’anin fasaha na kaf kasashen akalla 100.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel