Da Duminsa: Wata Kasar Turai Ta Dakatar Da Dokar Wajabta Yin Riga Kafin Korona

Da Duminsa: Wata Kasar Turai Ta Dakatar Da Dokar Wajabta Yin Riga Kafin Korona

  • Austria tana yunkurin dakatar da wajabta yin riga-kafin cutar COVID-19 ga manya kamar yadda gwamnatin kasar ta shaida a ranar Laraba
  • Kasar tana daga cikin kasashe kadan na duniya wadanda suka fara karya dokar wajabta yin allurar don kariya daga cutar coronavirus
  • A watan Fabrairu ta kafa dokar wacce tace matsawar mutum ya ki bin dokar za a ci shi tarar £3,600 ($3,940) tun daga tsakiyar watan Maris

Austria - Kasar Austria tana yunkurin dakatar da dokar wajabta yin riga-kafin cutar COVID-19 ga manya, inda a ranar Laraba gwamnatin ta bayyana hakan bayan wata daya da kafa dokar, The Punch ta ruwaito.

Kasar mai yawan mutane miliyan 9 tana daya daga cikin kasashen da suka fara kawo cikas ga dokar wajabta riga-kafin cutar coronavirus ga duk babba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Da Duminsa: Wata Kasar Turai Ta Dakatar Da Dokar Wajabta Yin Riga Kafin Korona
Da Duminsa: Austria Ta Dakatar Da Dokar Wajabta Yin Riga Kafin Korona. The Punch
Asali: UGC

A watan Fabrairu ta kafa dokar tare da cin tarar £3,600 ($3,940) ga duk wanda ya ki bin dokar daga tsakiyan watan Maris.

Ministan lafiya ya ce wannan nau’in cutar ba ta kai waccan tsanani ba

Sa dai minista Karoline Edtstadlee ya ce dokar ta ci karo da hakkin bil’adama wacce ba ta kai tsananin da za a hada ta da hatsarin annobar ba.

A cewarsa bisa ruwayar The Punch:

“Bayan tuntubar ministan lafiya, wajibi ne mu bi abinda kwararrun suka fadi. Mun lura da cewa babu bukatar wajabta amfani da riga-kafin saboda yadda wata nau’in cutar take kara yaduwa a nan.
“Ana saurin kamuwa da wannan nau’in amma ba ta kai hatsarin waccan ba. Don haka asibitocin Austria suna iya kulawa da cutar.”

Kara karanta wannan

Auran Sarauta: Sarkin Iwo zai angwance da jikar Sarkin Kano Ado Bayero, Firdausi

Dama mutane suna ta kira akan dage dokar cin tara ga wadanda suka ki riga-kafin

Ana ta kira akan duba akan dokar, musamman ganin yadda kasar ta kawo dokoki da dama akan coronavirus.

Daga ranar Talata, Austria ta kirga kusan mutane miliyan 3 da suka kamu da cutar sannan fiye da mutane 15,000 sun mutu tun daga farkon cutar a 2020.

Mahaifiyar ɗan majalsa ta rasu awa 24 bayan raba wa matan da mazajensu suka rasu kuɗi da kayan abinci

A wani rahoton, mahaifiyar Dan Majalisar Wakilai na Tarayya kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, a Jihar Anambra, Chuma Umeoji, ta rasu, rahoon The Punch.

Mahaifiyar dan majalisar, Ngozi Umeoji, ta rasu ne a ranar Lahadi, a kalla awa 24 bayan ta raba wa matan da mazajensu suka rasu shinkafa, kudi da kayan abinci a garinsu a Ezinifite, karamar hukumar Aguata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164