Da Dumi-Dumi: Dakarun Rasha sun zagaye birnin da Daliban Najeriya ke ciki a Ukraine

Da Dumi-Dumi: Dakarun Rasha sun zagaye birnin da Daliban Najeriya ke ciki a Ukraine

  • Akalla daliban Najeriya 370 dake karatu a ƙasar Ukraine suka makale a birnin Sumy yayin da Dakarun Rasha suka zagaye birnin
  • Sakataren Ofishin jakadancin Ukraniya a Najeriya yace ya kamata FG ta tashi tsaye matukar tana son ceton ɗaliban
  • Yace gwamnati ta tattauna da Rasha domin kada daliban su cutu yayin da aka shiga kwana na 7 da yaƙi

Kusan ɗalibai yan asalin Najeriya 370 ne suka maƙale a wani birnin ƙasar Ukraniya da Sojojin Rasha suka zagaye.

Daliban da suka maƙale a ciki na fuskantar barazanar cutarwa kasancewar dakarun Rasha sun kara zafafa kai hare-hare biranen Ukraniya a yaƙin da ya shiga rana ta 7 ranar Laraba.

Sakatare na biyu a ofishin jadancin Ukraniya a Najeriya dake Abuja, Bohdan Soltys shi ne ya faɗi haka yayin fira da Leadership ranar Laraba.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Zan Sayar Da Chelsea, Zan Ba Wa Mutanen Da Yaƙi Ya Ritsa Da Su A Ukraine Kuɗin, Abramovich

Rasha-Ukraine
Da Dumi-Dumi: Dakarun Rasha sun zagaye birnin da Daliban Najeriya ke ciki a Ukraine Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ya ce ɗaliban Najeriya dake cikin birnin Sumy sun maƙale, kuma babu wata hanyar fita daga birnin saboda sojojin Rasha sun zagaye shi baki ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma roki gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, musamman hukumomin jin kai su gaggauta yin wani abu domin tseratar da yan Najeriya daga mamayar sojojin Rasha.

A kalamansa ya ce:

"Jami'ar Sumy na ɗaya daga cikin jami'o'in da suka yi zarra a Ukraine kuma ta na da daruruwan ɗalibai yan Najeriya dake karatu a ciki."
"Dalibai 370 sun maƙale a cikin birnin saboda dakarun Rasha sun zagaye shi kuma babu wata hanyar fita daga ciki a yanzu."
"Ina ganin ya kamata a Ofishin jakadancin Najeriya a Ukraniya ya nemi FG ta tattauna a Rasha domin a samar wa daliban wata hanya su fita."

Wane mataki FG ke ɗauka na dawo da ɗaliban gida?

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Shugaba Buhari ya amince da dala miliyan $8.5m na kwaso yan Najeriya daga Ukraine

A halin yanzun shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince. da dala miliyan takwas da rabi domin aikin jigilar dawo da yan Najeriya da suka maƙale a kasar.

Gwamnati ta ce zata tura jiragen da zasu yi aikin kwaso mutane yau Laraba, kuma ana tsammanin sawu na farko za su iso gida gobe Alhamis.

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun sake kai mummunan hari, sun halaka dandazon mutane

Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun aikata mummunar ɓarna a kauyen Amangwu Ohafia dake yankin jihar Abia.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun halaka mutane ma su adaɗi mai yawa, wanda har yanzun ba'a gano yawan su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262