Gwanda mu mutu da mu koma Najeriya, Wasu yan Najeriyan dake kasar Ukraniya

Gwanda mu mutu da mu koma Najeriya, Wasu yan Najeriyan dake kasar Ukraniya

  • Yayinda gwamnati ke alkawarin kwashe yan Najeriya daga Ukraniya, wasu sunce dawowa Najeriya ci baya ne
  • Kimanin yan Najeriya 12,000 wanda da ya hada da mazauna da dalibai aka kiyasta suna kasar Ukraniya
  • Gwamnatin tarayya da majalisan wakilai sun yi alkawarin zuwa kwaso yan Najeriya gida

Wasu yan Najeriya dake zaune kasar Ukraniya yanzu haka sun yi watsi da maganar gwamnatin tarayya na kwasosu daga can sakamakon yakin kasar da Rasha

Daily Trust ta ruwaito wasu yan Najeriya na cewa sun gwammace yaki ta ci su da su dawo gida Najeriya.

Edidiong Cyprian Ukpakha, wani dan Najeriya da ya dade a birnin Kiev yace duk karyace maganar da gwamnatin Najeriya keyi, babu abinda za tayi saboda jirage yanzu ba sa tashi.

Hakazalika yace gwamnatin Najeriya ba ta cika alkawuranta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Faɗa Wa Rasha Ta Janye Sojojinta Daga Ukraine

Yace:

"Ina nan a 2013 lokacin wani rikici irin wannan kuma sukayi alkawarin kwashe yan Najeriya amma basu yi ba."
"Maganar gaskiya itace jirage ba su tashi yanzu, Amurka tuni ta kwashe yan kasarta, da sauran kasashe."

Gwanda mu mutu da mu koma Najeriya, Wasu yan Najeriyan dake kasar Ukraniya
Gwanda mu mutu da mu koma Najeriya, Wasu yan Najeriyan dake kasar Ukraniya
Asali: Facebook

Treasure Chinenye Bellgam, wani dalibi ya ce abinda gwamnatin Najeriya ke kokarin yi na da kyau amma,

"Mafi akasarin yan Najeriya kudi suka zo nema kuma ba zasu yarda su koma Najeriya ba, sun gwammace su mutu a nan."
"Kamar Allah ya daga ka ne amma kana son komawa baya, kamar koma baya (komawa Najeriya)."

Wani matashin Julius yace gaskiya yan Najeriya ba zasu yarda su koma gida ba.

Yace:

"Dubi ga yadda tattalin arzikin Najeriya yake, ina ga yawancin mutane zasu nemi wajen fakewa ne amma ba komawa Najeriya."

Kara karanta wannan

Rasha vs Ukraine: Ku Rufa Mana Asiri, Ku Ja Bakinku Ku Yi Shiru, 'Yan Najeriya Sun Shawarci FG

Gwamnatin Buhari Ta Faɗa Wa Rasha Ta Janye Sojojinta Daga Ukraine

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gana da wakilan kasashen G7 a Najeriya inda ta nuna damuwar ta game da rikicin Rasha da Ukraine tana mai kira da a warware lamarin cikin zaman lafiya, rahoto Daily Trust.

Ministan harkokin kasashen waje, Goeffrey Onyeama, ya gana da wakilan a ranar Juma'a a Abuja, yana mai cewa gwamatin Najeriya ta yi kira da a zauna lafiya kuma a yi amfani da diflomasiyya da wurin warware matsalar cikin lumana.

Onyeama ya ce Najeriya bata goyon bayan matakin da Rasha ta dauka na amfani da karfin soji, tana mai kira ga Rasha ta janye dakarunta, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng