'Karin Bayani: Dakarun Sojojin Ukraine Sun Harbo Jiragen Yaƙin Rasha 5 Tare Da Helicofta

'Karin Bayani: Dakarun Sojojin Ukraine Sun Harbo Jiragen Yaƙin Rasha 5 Tare Da Helicofta

  • Dakarun Sojojin kasar Ukraine sun harbo jiragen yaki guda biyar da helicofta daya mallakar kasar Rasha
  • Hakan na zuwa ne bayan dakarun na Rasha sun kaddamar da wasu hare-hare a wani yanki na Ukraine da taimakon Belarus
  • Mai magana da yawun hukumar tsaro na Ukraine ya ce akwai yiwuwar daruruwan sojojin Rasha sun rasa ransu sakamakon harin

Ukraine - Dakarun Sojojin Kasar Ukraine sun harbo jiragen yaki biyar da kuma helicofta mallakar kasar Rasha, rahoton Daily Trust.

Hakan na zuwa ne bayan harin da aka kai wa Ukraine din bisa umurnin Shugaba Vladmir Putin na Rasha.

Yanzu-Yanzu: Dakarun Sojojin Ukraine Sun Harbo Jiragen Yaƙin Rasha 5 Tare Da Helicofta
Dakarun Sojojin Ukraine Sun Harbo Jiragen Yaƙin Rasha 5 Tare Da Helicofta. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Hukumomi sun tabbatar da harin

Mai magana da yawun hukumar tsaro na Ukraine, a rahoton na Daily Trust ya ce akwai yiwuwar daruruwan sojojin Rasha sun mutu sakamakon harin.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Buhari ya dage rattafa hannu kan dokar zabe zuwa ranar Juma'a

Hukumar tsaron iyakokin Ukraine ita ma ta ce harin sojojin na Rasha ya zo ne daga Belarus da ke makwabtaka da su.

Hukumar ta ce dakarun na Rasha sun kaddamar da hare-hare tare da goyon bayan Belarus.

"Ana kai wa dakarun da ke iyakoki, da shinge hari ne ta hanyar amfani da manyan makaman soji, kayan yaki da kananan makamai. An kuma gano ayyukan makiya da kungiyoyi masu tattara bayanai halin da kasa ke ciki," a cewar sanarwar da hukumar ta fitar.

An fitar da sanarwar ne a lokacin da Ministan harkokin cikin gida na Ukraine ya sanar da faduwar garin Shchastya, wani gari da ke kudancin kasar da 'yan tawaye suka mamaye.

Harin na Rasha, a cewar rahotanni ya fada wa wani gida a kudancin Kharkiv, Ukraine.

Kara karanta wannan

Karya ne, ba'ayi gobara a ma'aikatar kudi ba, batir ne kawai ya kama da wuta: Ministar Kudi

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164