Kotu ta garkame magidanci a gidan yari bayan ya kara aure babu amincewar uwargidansa
- Wata kotu da ke kasar Pakistan ta aike wani magidanci gidan maza bayan ya kara aure babu amincewar matarsa
- Kotun lardin Lahore ta yanke wa Saqib wannan hukunci tare da cin tararsa dala dubu biyu duk da dokar kasar ta bashi damar kara aure
- Masu rajin kare hakkin mata sun yi murna da hukuncin inda suka ce hakan zai dakile masu cin amanar matansu
Wata kotu da ke zama a kasar Pakistan ta aike wani magidanci zuwa gidan yari sakamakon kara aure na biyu da yayi babu amincewar uwargidansa.
Kotun da ke zama a lardin Lahore ta yi fatali da ikirarin magidancin mai suna Shahzad Saqib na cewa addininsa na Musulunci ya bayar a damar ya kara aure, Aminiya Daily Trust ta rahoto.
Matar Saqib mai suna Ayesha Bibi, ta samu nasara a kotun bayan da ta yi ikirarin cewa kara auren da yayi babu amincewarta ya ki duba dokokin iyali na kasar Pakistan, al'amarin da yasa kotun ta ci tarar Saqib dala dubu biyu.
Masu rajin kare hakkin 'ya'ya mata, sun ce wannan hukuncin da kotun ta yanke zai karya guiwar maza masu niyyar kara aure ko kuma cin amanar matansu, kuma hakan tamkar bude wa mata kofar neman hakkinsu ne a gaban kuliya.
Sanannen abu ne a kasar cewa maza suna da damar auren mace fiye da guda, amma ya zama tilas matar farko ta amince kafin a kai ga daura auren ta biyun, Aminiya Daily Trust ta ruwaito.
A halin yanzu, Saqib ya na da damar daukaka kara zuwa kotun gaba kan hukuncin da aka yanke masa.
Majalisar harkokin addinin Musulunci ta kasar sun dade suna suka tare da caccakar wannan dokar ta iyali a kasar kuma suna bai wa gwamnati shawarwari da suka shafi harkokin addini.
Hotunan ango da amarya da basu kashe N50k a bikinsu ba, sun saka tsofaffin kaya
A wani labari na daban, wani mutum mai suna Gborienemi Mark- Charles, daga jihar Bayelsa, ya bayyana yadda ya kashe kasa da N50,000 a shagalin auren shi.
Kamar yadda Gborienemi ya bada labari, matarsa ce ta shawarce shi da kada ya barnata dukiyar shi a shagalin auren su, da haka gara ya narka a kasuwancin shi.
"Masoyina, ina rokon alfarma, a shagalin auren mu, ba na so ka barnata kudin ka wajen siyan rigunan amarya, abinci, abun sha, hayar wurin shagali, kwalliya da sauran abubuwan da basu taka kara sun karya ba. Da haka, gara ka kara kudin a kasuwancin ka"
Asali: Legit.ng