Satar kudi: Ni ne nan na taimaka aka saye gidaje, kamfanoni – Shaida ya fasa kwai a kotu
- Lauyoyin hukumar ICPC sun soma kiran shaidu su gabatar da hujjoji a shari’arsu da Dibu Ojerinde
- Wani lauyan tsohon shugaban na hukumomin JAMB da NECO, Peter Oyewole ya bada shaida a jiya
- Oyewole ya fadi yadda ya budewa mai gidansa kamfanoni, ya saya masa gidaje da hannun jarin banki
Abuja - Wani mai bada shaida da hukumar ICPC ta gabatar a kotun tarayya, ya zargi tsohon shugaban JAMB, Dibu Ojerinde da taba dukiyar gwamnati.
ICPC ta na shari’a da Dibu Ojerinde a babban kotun tarayya da ke garin Abuja. Premium Times ta ce ana tuhumar wannan mutum da laifin satar biliyoyin kudi.
Peter Oyewole wanda ya kasance Lauyan Ojerinde a lokacin da yake aiki da JAMB, ya bayyana a gaban Alkali a matsayin shaidan hukumar ICPC na farko a kotu.
Mista Oyewole ya fadawa kotu yadda ya taimakawa Ojerinde wajen buda wasu kamfanoni da kuma sayen hannun jari a lokacin da yake matsayin Lauyansa.
Shaidan da aka kawo ya ce Ojerinde ya bude kamfanoni takwas, ya saye gidaje uku da hannun jari a bankuna da sunan wasu mutane a sa’ilin yana rike da mukami.
A cewar Oyewole, bayan Ojerinde ya bar NECO, ya karbi shugabancin JAMB, ya zo da wasu tsofaffin ma'aikatansa da ke neman gidajen zama a garin Abuja.
Hakan ta sa shi lauyan ya nemo gidajen sama biyu da mara bene da aka saya a EFAB Properties Ltd. An saye gidajen da sunan lauyan, sannan ba a gama ginin ba.
Shari'a ta bi ta kan 'dan majalisa
Vanguard ta rahoto lauyan ya na fadawa Alkali cewa ya mika takardun gidajen a 2012 ga yaron wanda ake zargi, Hon. Olumide Ojerinde (yanzu ‘dan majalisa ne).
Kamfanonin da Ojerinde ya mallaka
Ya ce kamfanonin da Ojerinde ya mallaka a lokacin da yake rike da NECO da JAMB su ne: Oke-Afin Boys & Girls Hostel Limited, Sapati International School, Doyin Ogbohi Petroleum Limited.
Sai kuma Cheng Marbles Limited, Standout Institute Limited, Trillion Learning Center Limited, Grace Petroleum Limited da Ifelodun Communications Limited.
Mai shari’a, Obiora Egwuatu ya karbi takardun filaye da na mallakar kamfanoni a matsayin hujjoji. Sauran hujjojin da aka bada sun hada da takardun banki.
An yi amfani da wasu sunaye domin ayi wa kamfanonin rajista. Sunayen sun hada da; Ojerinde Dayo, Ojerinde Olumide, Awodayo Habib, da Adeyanju Gbenga.
Sai kuma Ojerinde Olutoyin, Ojerinde Akanbi, Ojerinde Adedayo, Olayiwola Ayanwale and Ibrahim Danmusa, Ojerinde Dibu, Sanusi Alade Najeem, da dai sauransu.
Gidaje sun sha ruwa?
Jaridar Premium Times ta ce kawo yanzu an karbe wasu gidajen wanda ake tuhuma a garuruwan Ilorin, Ibadan, Ogbomoso, Ile Ife da kuma birnin tarayya Abuja.
An nemi a sasanta a wajen kotu
A ranar Talata Lauyan da yake kokarin wanke Dibu Ojerinde, Ibrahim Ishyaku SAN ya nemi alfarmar a karasa shari’arsu a wajen kotun da ake shari'a a Abuja.
Sai dai hakan bai yiwu ba kafin jiya, kuma dama lauyan ya fadawa Alkali cewa za a iya cigaba da shari’ar idan har an gagara samun matsaya tsakaninsu da ICPC.
Asali: Legit.ng