Gwamnatin kasa ta haramtawa ma'aikata rungumar juna, Sunbata da kalaman batsa a wurin aiki

Gwamnatin kasa ta haramtawa ma'aikata rungumar juna, Sunbata da kalaman batsa a wurin aiki

  • Kasar Mexico ta hana ma'aikatan dake karkashinta aikata wani abu da ya shafi Jima'i kamar rungumar juna da sumbatar juna a wurin aiki
  • Wannan na kunshe ne a wasu sabbin dokokin da gwamnati ta fitar a hukumance ranar Talata, 8 ga watan Fabarairu 2022
  • Yayin da ake fuskantar ranar masoya ta duniya, dokokin sun hana ba da wata kyauta dake nufin sha'awar kwanciya

Mexico - Ƙasar Mexico ta hana ma'aikata maza da mata runguma da sunbatar juna, da kuma kyautar wani abu da ka iya tada sha'awa a wurin aiki.

Jaridar Punch ta rahoto cewa hakan na ƙunshe ne a wata sabuwar dokar Code Of Ethics da ƙasar ta saki ranar Talata, 8 ga watan Fabrairu da nufin shawo kan cin zarafi.

Shugaban ƙasar Mexico
Gwamnatin kasa ta haram ma'aikata rungumar juna, Sunbata da kalaman batsa a wurin aiki Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Waɗan nan sabbin dokokin na zuwa ne a dai-dai lokacin da zanga-zangar mata dake fafutukar kawo karshen cin zarafin mata ta hanyar jima'i ke ƙaruwa a sassan ƙasar.

Kara karanta wannan

Yan bindigan sanye da kayan sojojin Najeriya sun bindige wani shahararren dan kasuwa har lahira

Dokokin waɗan da aka buga su a jaridar gwamnati, ta umarci ma'aikata su guji, "Haɗa jiki a fili da zai tada sha'awa kamar taɓa jiki, rungumar juna, sunbatar juna."

Haka nan dokokin sun gargaɗi ma'aitan su guji, "Kalamai, wasanni ko wasannin ban dariya ga wani mutum na daban (Mace ko Namiji) game da shigarsa tare da nufin jima'i."

Shin akwai hukunci ga masu karya dokokin?

Sabbin dokokin sun fito ne ƙasa da mako ɗaya da ranar Masoya ta duniya (Valentines Day), kuma sun hana bayar da kyauta dake nuna sha'awar kwanciya da juna.

Kazalika duk wanda ya karya dokokin zai fuskanci hukunci dai-dai da abin da ya aikata kamar yadda yake ƙunshe a kundin dokokin gwamnatin Mexico.

A wani labarin kuma Muhimman abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da Jaruma Sadiya Haruna da Kotu ta ɗaure

Kara karanta wannan

Jaruma Sadiya Haruna, Rabi Isma'ila da wasu Jarumai Mata 2 da Kotu ta ɗaure a Kurkuku

Kotu a jahar Kano ta yanke wa Jaruma Sadiya Haruna hukuncin zaman gidan Yari na tsawon watanni 6 ba tare da zabin tara ba.

Mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa shida game da tsohuwar Jarumar wanda ka iya yuwu wa baku san da su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262