An kashe shugaban ISIS, Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi
- Joe Biden, shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa Shugaban kungiyar ISIS, Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi ya mutu
- Biden ya ce dakaru na musamman na kasar Amurka ne suka kai wata samame a gidan da Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi ya ke a Syria
- Shugaban na Amurka ya ce Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi ya yi amfani da rigar bam ya halaka kansa a yayin da ya lura ba shi da mafita
Shugaban Amurka, Joe Biden, a ranar Laraba, 3 ga watan Fabrairu, ya tabbatar da kashe shugaban Islamic State leader, ISIS, Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi, a wani samamen dare da Sojojin Amurka suka kai a arewa maso yammacin Syria, rahoton HumAngle.
Wata sanarwa da Shugaba Biden ya fitar ta ce:
"A daren jiya bisa umurni na, Dakarun Sojojin Amurka sun yi nasarar kai wata samame na mayar da martani ga masu aikata ta'addanci."
Ya kara da cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Mun kawar da Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi - shugaban ISIS daga filin daga."
A cewar wata rahoto da New York Times ta wallafa, kimanin dakarun sojojin Amurka 24 ne suka kai samamen, tare da helicofta masu bindigu, da jirgi mara matuki wato drone da jirgin yaki na jets.
Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi ya zama shugaba ne bayan mutuwar Abu Bakr al-Baghdadi
Shugaban na ISIS ya maye gurbin magabacinsa, Abu Bakr al-Baghdadi ne a watan Oktoban 2019 bayan samamen da aka kai a arewa maso yammacin Syria.
Yayin jawabinsa da ya yi da White House, tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Abu Bakr al-Baghdadi ya kashe kansa da yayansa uku ne bayan ya tada riga mai bam.
Bayan nadin al-Qurayshi da Kwamitin Shura tayi, rassan kungiyoyin ISIS duk sun masa mubaya'a har da na arewa maso gabashin Najeriya da Tafkin Chadi.
Zulum: Boko Haram za ta zama tamkar wasan yara idan aka bari ISWAP ta girma
A wani labarin, Farfesa Babagana Zulum, Gwamnan Jihar Borno, ya nuna damuwa game da kara karfi da kungiyar Islamic State in West African Province (ISWAP) ke yi, rahoton The Cable.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi game da mayar da yan hijira zuwa gidajensu da hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jiharsa a Abuja.
Tun a watan Janairu, Zulum ya yi gargadi cewa idan ba a dauki mataki game da ISWAP ba a Borno, 'ba mutanen yankin arewa maso gabas kawai zai shafa ba, kasar baki daya abin zai shafa.'
Asali: Legit.ng