Shugaba Buhari ya gana da shugaban kasar Guinea, sun magantu kan batun juyin mulki a kasar

Shugaba Buhari ya gana da shugaban kasar Guinea, sun magantu kan batun juyin mulki a kasar

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya magantu da shugaban Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo wanda sojoji suka yi yunkurin hambarar da gwamnatinsa
  • Shugaban Najeriyar ya yi Allah wadai da yunkurin juyin mulki a kasar ta Guinea Bissau, inda ya jinjinawa sojoji masu biyayya da suka nuna kishin kasa
  • Har ila yau Buhari ya ce ya yi farin ciki sosai da jin cewa abubuwa sun daidaita a kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi magana da shugaban kasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embalo, wanda sojoji suka yi yunkurin yiwa juyin mulki.

Buhari ne ya sanar da hakan a ranar Laraba, 2 ga watan Fabrairu, a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook.

Shugaba Buhari ya gana da shugaban kasar Guinea, sun magantu kan batun juyin mulki a kasar
Shugaba Buhari ya gana da shugaban kasar Guinea, sun magantu kan batun juyin mulki a kasar Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

A wallafar tasa, Buhari ya ce:

“Na yi magana da Umaro Sissoco Embalo, shugaban kasar Guinea Bissau.

Kara karanta wannan

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

“Na yi farin ciki matuka da na ji daga gare shi cewa an shawo kan lamarin kuma cewa komai lafiya yanzu; harkoki sun koma yadda suke a kasar.''
“Na taya shi murnar tsallake yunkurin juyin mulkin, kuma na yaba wa dakarun kasar masu biyayya kan kishin kasa da suka nuna wanda ya kaisu ga samun nasara a kan sojojin da suka yi tawaye.
“Yunkurin juyin mulki a Guinea Bissau abun Allah wadai ne gaba daya. 'Yan kasar Guinea-Bissau da gwamnatin Embalo za su ci gaba da cin moriya da samun goyon bayan gwamnati da al'ummar Najeriya.
“Ina zuba idon yin aiki tare da Shugaba Embalo da karfafa alakar da ke tsakanin kasashenmu, da kare da inganta damokradiyya da manufofinta a fadin yankin da nahiyar gaba daya."

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Yakamata arewa ya samar da magajin Buhari – Gwamnan PDP

An jiyo ƙarar harbe-harben bindiga kusa da fadar shugaban ƙasar Guinea

A baya mun ji cewa an jiyo ƙarar harbe-harbe na tashi a kusa da fadar shugaban ƙasa dake Guinea, babban birnin ƙasar Guine-Bissau ranar Talata.

The Cable ta tattaro cewa duk da har yanzun ba'a gano musabbabin harbe-harben ba, amma Dakarun sojojin ƙasar sun zagaye fadar yayin da shugaban ƙasa, Umaro Sissoco Embaló, ke gudanar da taro da yan majalisar zartarwansa.

Tun bayan da ƙasar ta samu yancin kai daga ƙasar Portugal a 1974, Guinea-Bissau ta sha fama da juyin mulki kala daban-daban, tawayen sojoji da kuma yi wa yan siyasa kisan gilla.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng