Karshen Korona: Jirgi zai fara jigila daga Dubai zuwa Najeriya ranar 5 ga wata

Karshen Korona: Jirgi zai fara jigila daga Dubai zuwa Najeriya ranar 5 ga wata

  • Kamfanin jirgin saman Emirates na kasar Dubai ya bayyana lokacin da zai ci gaba da safarar mutane tsakanin Najeriya da Dubai
  • Kamfanin ya bayyana hakan ne kwanaki kadan bayan dage dokar hana shiga ga 'yan Najeriya a kasar ta Dubai
  • Kamfanin ya kuma bayyana ka'idojin da za a cika a yayin da ake ci gaba da shirin fara zirga-zirgar

Dubai - Kamfanin jiragen sama na Emirates, mai jigilar mutane daga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), ya ce zai ci gaba da zirga-zirgar fasinjoji tsakanin Dubai da Najeriya a ranar Asabar 5 ga Fabrairu, 2022.

Kamfanin jirgin ya ce fasinjojin da ke tafiya zuwa Dubai za su yi karin gwajin cutar Korona kuma za su yi zaman kebe kansu har sai an karbi sakamakon gwajin, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Za'a shirya Fim na musamman kan Hanifa Abubakar, yarinyar da aka kashe a Kano

Jirgin Dubai na Emirates
Karshen Korona: Jirgi zai fara jigila daga Dubai zuwa Najeriya ranar 5 ga wata | Hoto: aljazeera.con
Asali: Getty Images

A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, kamfanin jirgin ya ce matafiya da ke zuwa daga Najeriya dole ne su rike takardar shaidar gwajin Korona da sa'o'i 48 kafin tashi.

Da wannan, an fahimci cewa fasinjoji daga Najeriya za su bukaci yin gwajin Korona ta PCR cikin kwanaki biyu kafin tashi.

Ya ce dole ne a sami takardar shaidar gwajin daga wurin da aka amince da shi kuma ya kunshi lambar QR domin tantance gaskiyar gwajin.

Bayan isa Dubai, fasinjoji kuma za su yi karin gwajin Korona na PCR kuma su kasance a kebe har sai sun karbi sakamakon gwajin.

Fasinjojin da ke tafiya daga Najeriya zuwa Dubai ana bukatar su bi ka'idoji da sharuddan tafiye-tafiye.

Emirates ta kara da bayyana cewa tun lokacin da ta dawo da harkokin yawon bude ido cikin aminci a watan Yulin 2020, Dubai ta kasance daya daga cikin shahararrun wuraren hutu a duniya, musamman a lokacin hunturu, Tribune ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Mutane sun mutu a wani sabon Hatsarin Jirgin ruwa da ya sake aukuwa a Kano

A wani labarin, an tabbatar da mutuwar mutum biyu a wani sabon hatsarin kwalekwalen gargajiya da ya auku a kauyen Zangon Durgu, karamar hukumar Rimin Gado, jihar Kano.

Kakakin hukumar kwana-kwana ta jihar, Saminu Yusif Abdullahi, shi ne ya tabbatar da haka ga manema labarai, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Yace Kwalekwalen, wanda ya dauko mutum hudu kacal, ya kife ne yayin da yake kan hanyar zuwa kauyen Kanya daga Zangon Durgu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.